Kogi: Dino Melaye ya yi ikirarin an kai masa hari ana kuma neman kashe shi

Kogi: Dino Melaye ya yi ikirarin an kai masa hari ana kuma neman kashe shi

- Sanata Dino Melaye ya godewa Ubangiji bayan ya tsallake tarkon wasu Miyagu

- Tsohon Sanatan ya ce an kai masa hari za a kashe shi ne a gaban wata makaranta

- ‘Dan siyasar ya ce wadannan miyagun mutane sun kashe Maigidansu madadinsa

A karshen makon nan ne Sanata Dino Melaye ya fito ya ba Duniya labarin yadda ya tsallake tarkon wasu mutane da su ka yi yunkurin gann karshen rayuwarsa.

Dino Melaye ya ce an kai masa hari za a kashe shi ne a gaban makaramtar nan ta koyon aiki ta jihar Kogi watau Kogi Polytechnic a ranar Lahadi, 31 ga watan Mayu.

Melaye ya bada wannan labari ne a shafinsa na zumunta na tuwita @dino_melaye. Shararren ‘dan siyasar ya bayyana cewa Ubangiji ne ya tsaga masa gyadar doguwa.

“Na godewa Ubangiji da wannan rana. Yau ce ranar da masu kisan-kai su ka nemi rayuwata a gaban makarantar Kogi State Polytechnic.” Inji @dino_melaye a tuwita.

KU KARANTA: Melaye ya kai Minista, Shugaban 'Yan Sandan Najeriya gaban Alkali

Fitaccen ‘dan adawar gwamnatin na APC mai-ci ya kara da cewa: “Maimakon su kashe ni, shugaban gungun miyagun, Saka ya mutu. Ubangiji ya cika Ubangiji."

Melaye ya cigaba da godiya, ya na kiran sunan Ubangiji da yarukan Hausa, Ibo da kuma Yoruba. Ya rubuta: “Oluwa seun. Chineke edima. Nagode Ubangijin Duniya.”

Ba wannan ba ne karon farko da Dino Melaye ya fito ya na cewa ana neman ganin bayan rayuwarsa. Kawo yanzu ‘yan sanda ba su tabbatar da wannan zance ba.

A 2017, Dino Melaye ya ce an harbi motocinsa lokacin da wasu tsageru su ka shigo gidansa da ke Ayetoro-Gbede a karamar hukumar Ijumu, jihar Kogi cikin tsakar dare.

Haka zalika daf da zaben 2019, mai magana da yawun bakin jam’iyyar PDP a jihar Kogi ya fito ya na cewa wasu miyagu su na kokarin hallaka Sanatan na Kogi ta yamma.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel