Babu dawowa baya game da ‘yancin majalisa da bangaren shari’a – Hadimin Buhari

Babu dawowa baya game da ‘yancin majalisa da bangaren shari’a – Hadimin Buhari

- Shugaba Buhari ya yi magana game da ba Majalisa da bangaren shari’a ‘yanci

- Hadimin Shugaban kasa, Sanata Ita Enang ya ce dokar EO-10 za ta tsaya kam

- Fadar Shugaban kasa ta na da ra’ayin da ya zo akasi da na Gwamnonin Jihohi

Fadar shugaban kasa ta ce babu batun komawa baya kan shirin dabbaka sabuwar dokar da shugaba Muhammadu Buhari ya kawo wanda ta karfafa majalisar dokoki da bangaren shari’a.

Babban mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin Neja-Delta, kuma sakataren dabbaka dokar shugaban kasa ta 10, Sanata Ita Enang, ya jaddada wannan a karshen makon nan a Garin Abuja.

Jaridar Daily Trust ta rahoto Sanata Ita Enang ya na cewa shi da shugaban kwamitin wannan aiki watau ministan shari’a, Abubakar Malami su na kokairn ganin an tabbatar da sabuwar dokar.

“Tun da dokar ba ta aiki, ina nufin garambawul din da aka yi a 2017, 2018, da 2019, shugaban kasa ne mai cikakken ikon kare hakin duk wani ‘dan Najeriya a kowane mataki na gwamnati.”

KU KARANTA: Gwamnoni ba su goyon bayan E0-10 da Buhari ya rattabawa hannu

Babu dawowa baya game da ‘yancin majalisa da bangaren shari’a – Hadimin Buhari
Ita Enang tare da Muhammadu Buhari. Hoto: @NgrPresidency
Asali: UGC

Enang ya ce kwaskwarimar da aka yi wa dokar kasa ta ba Muhammadu Buhari kasa damar kafa kwamiti da zai tabbatar majalisar dokokin jihohi da bangaren shari’a sun samu gashin kansu.

An amince da dokar ne a 2017 inda aka yi wa sashe na 121 (3) na tsarin mulki garambawul, hakan ya bada damar kudin majalisa da kuma bangaren shari’a su shiga hannunsu kai-tsaye a jihohi.

Babban hadimin shugaban kasar ya ce rashin bin wannan doka ta sa Muhammadu Buhari ya kawo yadda za a tabbatar da dabbaka cikakken ‘yancin ‘yan majalisar jihohi da malaman shari’a.

Sauran ‘yan wannan kwamiti bayan Malami SAN da Enang, sun hada da manyan Alkalan kotun shari’a na Gombe da birnin tarayya, shugaban NBA, kakakin majalisar Legas da wasunsu.

A baya Legit.ng Hausa ta rahoto cewa gwamnoni su na ganin wannan doka ta shugaban kasa wanda ta karbe iko daga hannunsu, ta ba sauran bangarori ‘yanci ta sabawa tsarin mulki.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel