Zamfara: Matawalle ya samar da 'yan sandan sa kai a jihar Zamfara

Zamfara: Matawalle ya samar da 'yan sandan sa kai a jihar Zamfara

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya amince da samar da 'yan sandan sa kai wadanda za su dinga aiki a karkashin kulawar jami'an 'yan sandan Najeriya da ke jihar.

Kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta wallafa, a wata takarda da mai bada shawara ta musamman ga Matawalle a kan yada labarai, Zailani Bappa ya fitar, ya ce sabuwar cibiyar tsaron za ta tattara 'yan sa kai daga kananan hukumomi 14 na fadin jihar.

Kamar yadda Bappa ya bayyana, za a horar da 'yan sa kan ne a hukumar 'yan sandan Najeriya.

Zamfara: Matawalle ya samar da 'yan sandan sa kai a jihar Zamfara
Zamfara: Matawalle ya samar da 'yan sandan sa kai a jihar Zamfara Hoto: The Interview Magazine
Asali: UGC

"Za a zaba matasa 700 don wannan aikin, 50 daga kowacce cikin kananan hukumomi 14 na jihar.

"Wannan sabon tsarin ya banbanta da tsohon tsarin 'yan sa kai na wadanda ke ruda al'amuran tsaro a baya.

"Sabon tsarin zai kunshi 'yan sa kai wadanda za a tantance kuma a horar da su karkashin hukumar 'yan sandan Najeriya kuma za a basu kayan aiki don a gano su da wuri.

"Aikinsu shine taya 'yan sandan Najeriya aiki a yankunansu," takardar tayi bayani.

Bappa ya ce tuni aka fara shirin kuma za a rantsar da kashin farko na 'yan sa kan nan babu dadewa.

KU KARANTA KUMA: Bauchi: Manema labarai basu fahimceni ba a kan silar mace-mace - Dr Mohammed

A wani labari na daban, mun ji cewa rundunar 'yan sandan jihar Legas ta ce ta kama sifetan dan sandan da ya halaka abokin aikinsa har lahira.

A wata takarda da ta fito a ranar Lahadi, Bala Elkana, jami'in hulda da jama'a na 'yan sandan jihar, ya ce Monday Gabriel ya dinga harbi wanda ya janyo mutuwar Felix Okago, dan sanda mai mukamin sajan.

Ya ce an sauya wa Gabriel wurin aiki ne daga Abuja zuwa Ikoyi ta jihar Legas don yin aiki na musamman. Jami'in hulda da jama'a na 'yan sandan jihar ya ce lamarin ya faru wurin karfe 4:30 na safe bayan ya illata mutane masu yawa.

Ya ce an kama sifetan dan sandan a yayin da yake niyyar tserewa ta gada ta uku a birnin Legas.

Elkana ya ce an fara bincike a kan aukuwar lamarin yayin da ake duba lafiyar kwakwalwar dan sandan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel