Roger Federer ya kerewa Lionel Messi da Cristiano Ronaldo a albashi - Forbes

Roger Federer ya kerewa Lionel Messi da Cristiano Ronaldo a albashi - Forbes

- ‘Dan wasan nan Roger Federer ya kafa sabon tarihi a harkar wasannin Duniya

- Gwanin Tanis, Federer ya samu kusan Naira Biliyan 40 a cikin shekarar 2019

- Kudin da Tauraron ya samu ya zarce na ‘Yan wasa Ronaldo, Messi da Neymar

‘Dan wasan Tanis na kasar Switzerland, Roger Federer ya yi wa Cristiano Ronaldo da su Lionel Messi fintinkau a sahun ‘yan wasan da su ka fi kowane albashi a shekarar bara.

A wani rahoto da aka fitar a mujallar Forbes, an fahimci cewa Roger Federer ya tsallake ‘yan wasa hudu a sahun attajiran Duniya bayan da ya samu fam dala miliyan 106.3 a 2019.

Federer ya zama ‘Dan wasan Tanis na farko a Duniya da ya taba rike wannan kujera a tarihi. Tauraron ya sha gaban manyan ‘yan asa irinsu Ronaldo, Messi da LeBron James.

Tallar da Federer ya yi wa kamfanoni a shekarar da ta gabata ta sa aljihunsa ya kumbura. Bayan haka kuma ‘dan wasan ya shiga manyan gasar da aka yi a kasashen Amurka.

KU KARANTA: Za a dawo wasan kwallon kafa a Ingila bayan lafawar COVID-19

“Annobar Coronavirus ta jawo an ragewa ‘yan wasan kwallon kafa irinsu Messi da Ronaldo albashi, wanda hakan ya budawa ‘dan wasan tanis kofar kafa tarihi.” Inji Forbes.

A kudin Najeriya, abin da Roger Federer ya tashi da shi a shekarar da ta gabata ya haura Naira biliyan 38,750,000,000.00. A shekarar badi ne Federer zai cika shekaru 40 a Duniya.

Wadanda su ka biyo bayan Federer su ne Ronaldo ($105m), Messi ($104m), sai kuma Neymer ($95.5m). ‘Dan wasan kwallon kwando, LeBron James ya zo na biyar da ($88.2m).

A Duniyar mata kuma mujallar ta Forbes ta rahoto cewa Naomi Osaka ba ta da tamka a halin yanzu. A tsakanin wannan lokaci ‘yar wasar ta mallaki dala fam miliyan 37.4.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng