Yanzu Yanzu: Gwamna Tambuwal ya gana da shugaba Buhari

Yanzu Yanzu: Gwamna Tambuwal ya gana da shugaba Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal kan matsalolin tsaro da aka samu kwanan nan a karamar hukumar Sabon Birni da ke jihar.

Tuni dai shugaba Buhari ya yi umurnin tura wata runduna ta sojoji yankin domin hana 'yan bindigar sakat a yankin.

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da hadimin Shugaban kasar, Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na twitter.

Ya ce: “Shugaba Muhammadu da ranan nan a fadar Shugaban kasa, Abuja, ya gana da gwamnan jihar Sokoto, Mai girma Aminu Waziri Tambuwal kan matsalolin tsaro da aka samu kwanan nan a karamar hukumar Sabon Birni da ke jihar. Tuni Shugaban kasar ya yi umurnin kaddamar da aikin sojoji a jihar da sauran wurare.”

A baya mun kawo cewa, Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya shirya tattaunawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan kisan gillar da 'yan bindiga ke yi wa jama'ar jihar sa, jaridar The Punch ta ruwaito.

A wata takarda da ta fito daga mai bada shawara kan yada labarai ga Gwamna Tambuwal, Muhammad Bello, ya ce, "Na tuntubi fadar shugaban kasa kuma na samu dama zan zanta da shi daga yanzu zuwa koyaushe.

"Da izinin Allah zamu tattauna a kan rashin tsaro da ya addabi sashin kudu maso gabashin jihar nan. Za mu tattauna a kan yadda za a kawo karshen matsalar."

Gwamnan ya jaddada cewa an tura hukumar kula da al'amuran gaggawa zuwa yankunan da mummunan lamarin ya faru don rage radadi ga jama'a.

"Na umarci hukumar taimakon gaggawa da ta garzaya yankin don duba yanayin barnar da aka yi tare da rage radadi ga mazauna yankin," ya kara da cewa.

Ya yi addu'ar neman gafara ga mamatan tare da kira ga mazauna yankin da suka kiyaye da kuma gujewa daukar doka a hannunsu komai munin abinda zai faru.

KU KARANTA KUMA: Kotu ta yanke wa fasto hukuncin kisa ta hanyar rataya

A gefe guda mun ji cewa, sakamakon harin da 'yan bindiga suka kai garin Sokoto wanda yayi ajalin rayuka 70, wata kungiyar 'yan jihar Sokoto ta yi kiran gaggawa ga gwamnati a kan ta dauka mataki da wuri.

Kungiyar ta bayyana cewa, daga watan Janairun da ya gabata, a kalla an rasa rayuka 270 a jihar sakamakon hare-hare 20 da 'yan bindiga suka kai jihar.

A yayin jawabi ga manema labarai a madadin kungiyar, Farfesa Nasiru Gatawa ya ce sun cikin matsanancin hali don haka suna bukatar gwamnati ta dauka matakan gaggawa.

Kamar yadda yace, "muna da kananan hukumomi 8 a yankin gabas din jihar. Sun hada da: Gada, Goronyo, Gwadabawa, Illeila, Issa, Rabbah, Sabon Birni da Wurno.

"Yankin da aka fi takura wa shine Sabin Birni. 'Yan bindigar na kai kawo yadda suke so da rana tsaka ba tare da wani yunkurin hana su ba daga gwamnati.

"Kowacce daga cikin kananan hukumomin na karkashin 'yan ta'adda don sun gurgunta tattalin arzikinsu tare da asarantar da rayuka da kadarori," yace.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel