Manyan kabilu 10 da suka fi shahara a nahiyar Afrika
Ubangiji ya albarkaci nahiyar Afrika da mutane hazaikai da kuma kabilu masu tarin yawa.
Legit.ng ta tattara muku kabilu daban-daban da suka fi jama’a masu tarin yawa a nahiyar Afrika.
Ga jerin kabilu 10 a nahiyar Afrika da suka fi kowacce kabila yawa kamar yadda Facts one ta bayyana.
1. Kabilar Hausa - miliyan 78:
Tana da mutane a kalla miliyan 78 a fadin nahiyar Afrika. Ana samu masu yin yaren a kasashe masu tarin yawa na fadin haiyar.
2. Igbo - miliyan 45:
Da mutum miliyan 45 ne kabilar Ibo ta zama ta biyu a cikin kabilu mafi yawan mutane a nahiyar Afrika.
3. Yoruba - miliyan 44:
Kabilar nan ce ke biye da kabilar Ibo a yawan mutane a nahiyar Afrika. Tana da mutane masu yawan miliyan 44.
4. Oromo - miliyan 40:
Kabilar Oromo ce kabila ta hudu a yawan jama’a a nahiyar Afrika. Tana da mutum miliyan 40.
5. Fulani - miliyan 35:
Kabilar Fulani ce ta biyar a wannan jerin, tana da mutane miliyan 35 a nahiyar Afrika.
6. Amhara - miliyan 20.2:
Kabilar ce ta shida a wannan jerin kuma tana da jama’a miliyan 20.2
7. Akan - miliyan 20:
Akan kabila ce da ke da yawan mutane har miliyan 20 a fadin nahiyar Afrika.
8. Somali - miliyan 20:
Kabilar Somali c eke biye da Akan wacce ke da miliyan 20 na jama’a.
9. Hutu - miliyan 18.5:
Kabilar tana da jama’a miliyan 18.5 na masu yin yarenta a Afrika.
10. Ijaw - miliyan 15:
Kabilar Ijaw ce ta karshe kuma ta goma a wannan jerin. Tana da mutane miliyan 15 da ke yin yaren a Afrika.
KU KARANTA KUMA: Buhari ya yi garambawul a rundunar 'yan sanda, ya kirkiri sabbin kwamand 5
A baya mun kawo cewa, yaren Hausa ne yaren da aka fi yi kuma mafi dadewa a cikin yankin mutane miliyan 120 kamar yadda aka gano.
Masu yin yaren na nan dankam a kasashen Najeriya, Nijar, Chadi, jamhuriyar Benin, Kamaru, Togo, jamhuriyar Afrika ta tsakiya, Ghana, Sudan, Eritrea, Guinea, Gabon, Senegal da Gambia.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng