Tsaro: N7bn ce masu garkuwa da mutane suka karba cikin shekaru 9 a Najeriya
A Najeriya, garkuwa da mutane don karbar kudin fansa ya zama ruwan dare a sassan kasar daban-daban. An yi garkuwa tare da karbar kudin fansa daga dubban jama'a a kasar.
Tsakanin shekarar 2011 da 2020 a Najeriya, a kalla an biya biliyan 7 a matsayin kudin fansa kamar yadda rahoto a kan garkuwa da mutane na kasar nan ya bayyana.
Rahoto da kungiyar bincike ta SB Morgen ta wallafa a farkon watan Mayu, ta wallafa yawan garkuwa da mutane da aka yi daga watan Yunin 2011 zuwa Maris din 2020.
Rahotan ya kunshi sunaye, rana, jiha, yawan mutane da aka yi garkuwa dasu da kuma kudin fansa da aka biya.
KU KARANTA KUMA: COVID-19: Cutar Korona ta bulla jihar Kogi a karon farko

Asali: UGC
Kamar yadda SBM ta bayyana, jihohi 4 cikin 10 ne ke da tarin yawan wadanda aka yi garkuwa dasu kuma duk suna yankin kudancin kasar.
Jihohin su ne: Bayelsa wacce aka yi garkuwa da mutum 85, jihar Delta mai mutum 96 da Ribas mai mutum 120.
Sauran sun hada da jihar Kaduna mai mutum 177, jihar Borno mai mutum 82, jihar Kogi mai mutum 59, jihar Edo mai mutum 55, jihar Ondo mai mutum 54, Katsina mai mutum 52 sai Taraba mai mutum 47.
"Ya bayyana cewa an fi garkuwa da mutane a yankin Kudu. An fi zabar 'yan kasuwa ta yadda ake samun makuden kudade," wani sashi na rahoton ya bayyana.
"Wadanda suka kasa biya kudin fansa da aka yanke musu an fi gaggawar kashe su har lahira," rahoton ya kara sa cewa.
KU KARANTA KUMA: COVID-19: An bukaci gwamnoni su dena tsangwamar almajirai
Rahoton ya bayyana cewa, har zuwa kusan karshen 2018, ana duba 'yan siyasa, 'yan kasuwa da sauran masu hannu da shuni wajen yin garkuwa da jama'a.
"Yawaita harin 'yan bindiga a kauyukan Zamfara da Katsina ya sake assasa yawan garkuwa da mutane da ake yi. Lamarin da ya kai har jihohin Kaduna da Niger.
"Wadannan 'yan bindigar ne suke fitowa tituna don tare matafiya tare da yin garkuwa da su don neman kudin fansa," rahoton yace.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng