Gwamna Akeredolu ya bada damar a koma salloli da ibada a Jami’i a karshen mako

Gwamna Akeredolu ya bada damar a koma salloli da ibada a Jami’i a karshen mako

- Gwamnatin Jihar Ondo ta ce za a cigaba da bautar Ubangiji a cikin taro

- Rotimi Akeredolu bai bada damar yin ibada ta yau da kullum ba tukuna

- Za a rika buda masallatai da coci a duk ranakun Juma’a da kuma Lahadi

Gwamnatin jihar Ondo ta zare takunkumin da ta sa na haramta buda dakunan ibada. A halin yanzu, gwamna Rotimi Akeredolu ya bada sanarwar cewa za a bude wuraren bauta.

Mai girma Rotimi Akeredolu sanar da wannan ne sa’ilin da ya yi hira da ‘yan jarida a garin Akure, jihar Ondo. An yi wannan ganawa ne a jiya ranar Laraba, 27 ga watan Mayu, 2020.

Rotimi Akeredolu ya ce gwamnati ta dauki matakin bude masallatai da coci ne bayan ta yi zama da malaman addini da sauran masu ruwa da tsaki da ta cewa a fadin jihar Ondo.

A wajen wannan tattaunawa da manema labarai ne gwamnan ya sanar da mutuwar wani wanda ke jinyar ciwon COVID-19, wanda shi ne mutum na biyu da cutar ta kashe a jihar.

“Coci za su yi aiki a ranakun Lahadi, yayin da za a bude masallatai a ranakun Juma’a. Don haka na bada umarni a dawo bauta a cikin jami’i a duk dakunan ibadan da ke jihar Ondo.”

KU KARANTA: Gwamna Wike ya bude Jihar Ribas, ya soke takunkumin kulle

“Kamar yadda aka cinma yarjejeniya karara da shugabannin addini, za a fara bude wuraren ibada ne daga ranar Juma’ar nan. Amma kuma cire takunkumin ya na da kaidi.”

Gwamnan ya ce masu bauta za su bi sharudan da aka kafa domin takaita yaduwar COVID-19 a Najeriya. Gwamnati ba ta amince a rika bude wuraren ibada kullum ba tukuna.

Daga cikin dokokin da za a bi akwai wanke hannuwa da gujewa cinkoso da amfani da kariyar fuska. Gwamnan ya ce da haka a za takaita yada cutar COVID-19 a wuraren ibadan.

Akeredolu ya shaidawa mutanensa cewa: “Dabbaka tsarin dawowar zai zamana sannu a hankali cikin tsari.” A jiya an samu mutum guda da ya kamu da wannan cuta a jihar ta Ondo.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel