Ekiti: Ba mu maraba da Segun Oni a cikin Jam’iyyar PDP inji Ayo Fayose

Ekiti: Ba mu maraba da Segun Oni a cikin Jam’iyyar PDP inji Ayo Fayose

- Ayo Fayose ya na kokarin hana wani tsohon Gwamnan Ekiti sauya sheka

- Segun Oni ya na neman barin Jam’iyyar APC mai mulki ya dawo cikin PDP

- Tsohon Gwamnan Ekiti, Fayose ya ce Jam’iyyyar PDP ba ta lale da zuwansa

Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Peter Fayose, ya fito ya na cewa jam’iyyar PDP ba ta lale maraba da dawowar tsohon shugaban jam’iyyar APC, Injiniya Segun Oni.

Mista Ayodele Fayose ya bayyana Segun Oni da mutumin da bai da nauyi a siyasa, don haka ya nuna rashin goyon bayansa ga sauya shekar ‘dan siyasar da ya mulki Ekiti.

Fayose ya bayyana wannan ne a lokacin da ya ke maida martani game da wata wasika da Segin Oni ya rubutowa shugabannin PDP ya na sha’awar dawowa cikin tafiyarsu.

A ranar 24 ga watan Mayu, 2020, Oni ya aikowa shugabannin rikon kwarya na jam’iyyar PDP na Ekiti takarda, ya na shaida masu cewa zai sauya-sheka daga jam’iyyar APC.

KU KARATA: Rigingimu na neman mirginowa Jam’iyyar PDP kafin zaben 2023

Ekiti: Ba mu maraba da Segun Oni a cikin Jam’iyyar PDP inji Ayo Fayose
Ayo Fayose Hoto: Nairaland
Asali: UGC

Segun Oni wanda ya rike mataimakin shugaban jam’iyyar APC na kasa ya fice daga jam’iyyar ne kwanakin baya. Oni ya koka da cewa ba a ganin mutuncinsa a tafiyar APC.

Yunkurin komawa PDP ya tado tsohuwar gabar da ke tsakanin Fayose da Oni, wanda dukkaninsu sun rike gwamna a jihar Ekiti kuma duk a karkashin PDP mai hamayya a yau.

Fayose da kansa ne ya jefa wasikar Oni a shafin PDP na WhatsApp inda ya kira abokin gaban na sa da ‘dan siyasar da bai da nauyi kamar yadda jaridar This Day ta rahoto.

“Mafi yawan yaran Oni da su ke dawowa, ba su da nauyin komai, sunaye ne kawai na mutanen da ke neman shahara da son a sansu. Ba mu maraba da zuwansu.” Inji Fayose.

A gefe guda, bangaren jam’iyyar PDP na sanata Biodun Olujimi sun ji dadin wannan labari, kuma sun nuna za su fita su tarbi Oni da hannu biyu-biyu domin karawa APC karfi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel