Wike ya sassauta dokar zaman-gida da takaita zirga-zirga a Jihar Ribas

Wike ya sassauta dokar zaman-gida da takaita zirga-zirga a Jihar Ribas

- Gwamnatin Ribas ta cire takunkumin kullen da ta kakaba a wasu wurare

- Gwamna Nyesom Wike ya dauki sababbin matakan yaki da Coronavirus

- Duk da haka gwamnan ya ce babu wanda zai shiga jihar sai ta zama dole

Mai girma gwamna Nyesom Wike ya cire takunkumin zirga-zirga da ya sa a wasu garuruwa da su ka hada da Obio, Akpor da kuma babban birnin jihar Ribas na Fatakwal.

Kwanakin baya gwamnan ya kafa dokar zaman gida domin gujewa yaduwar cutar COVID-19. Jaridar The Nation ta ce yanzu gwamnatin Ribas ta sassauta wannan doka.

Gwamna Nyesom Wike ya bada wannan sanarwa ne a ranar Talata, 26 ga watan Mayu, 2020. Hakan na zuwa ne jim kadan bayan musulmai sun yi bikin karamar sallah.

Gwamnatin Ribas ta kuma haramta fita waje daga tsakanin karfe 8:00 na dare zuwa 6:00 na yamma. Wannan sabuwar doka za ta fara aiki ne daga ranar Talata mai zuwa.

KU KARANTA: Ma'aikata sun hurowa Gwamnan Kano wuta a kan rage albashi

Wike ya sassauta dokar zaman-gida da takaita zirga-zirga a Jihar Ribas
Gwamnan Jihar Ribas Nyesom Wike Hoto: Facebook
Asali: Twitter

Da ya ke yi wa mutanen jihar Ribas jawabi, gwamnan ya ce sun dauki wannan mataki ne bayan sun duba sha’anin da fuskar basira, ya kuma wajabtawa kowa rufe fuska.

“Bayan dogon la’akari da matakin da aka dauka da kuma korafin da mutanen kwarai su ke yi da al’umma, majalisar tsaro da cire takunkumin kullen da ta sa.” Inji gwamnan.

Ya ce: “A dalilin haka, babu wani bangare na jihar Ribas da zai zama cikin takunkumi a wannan lokaci, kuma haka za a cigaba har sai lokacin da bukatar hakan ta sake tashi.”

Gwamnan ya ce babu ranar bude gidajen disko, wuraren rawa da kallon wasanni fina-finai, da dakunan shan giya. Haka zalika duk wata kasuwa da ta ke fili ba za ta ci ba.

Dole kowa ya rufe fuskarsa idan har zai fita waje domin gujewa fadawa hannun hukuma. Iyakokin jihar za su cigaba da zama a rufe idan ba ga masu kwararran dalili ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel