Gwamnatin Kano ta kafa wuraren karbar samfur 9 na gwajin coronavirus a jihar

Gwamnatin Kano ta kafa wuraren karbar samfur 9 na gwajin coronavirus a jihar

Gwamnatin jihar Kano ta kafa wuraren karbar samfur tara na gwajin coronavirus a jihar don hanzarta shawo kan muguwar annobar, jami'ai suka sanar.

Tijjani Hussaini, shugaban kwamitin yaki da annobar Coronavirus a jihar, ya sanar da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya hakan a ranar Laraba, 27 ga watan Mayu, a Kano.

Hussaini ya ce takwas daga cikin wuraren karbar samfur din an kafa su ne a cikin birnin Dabo yayin da daya ke karamar hukumar Rano ta jihar.

Gwamnatin Kano ta kafa wuraren karbar samfur 9 na gwajin coronavirus a jihar
Gwamnatin Kano ta kafa wuraren karbar samfur 9 na gwajin coronavirus a jihar Hoto: Ripples Nigeria
Asali: UGC

"Nan ba da jimawa ba za a kafa dakunan karbar samfur 10 inda jimillar zai koma 19 a fadin jihar.

"Muna ci gaba da karbar masu aikin sa kai a dukkan kananan hukumomin jihar don assasa binciko masu cutar.

"Tsarin shine kafa dakunan karbar samfur a kowacce karamar hukumar jihar," yace.

Hussaini ya ce hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa ta Najeriya ta kafa dakunan gwaji uku a jihar.

Ya ce gidauniyar tallafi ta Dangote ta kafa dakin gwaji a asibitin Muhammadu Buhari da ke Giginyu.

"Dakin gwajin na iya gwada samfur 650 a rana daya. Ana kokarin kai yawan gwajin zuwa 1,300 da 1,500 a kowacce rana," yace.

Shugaban ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta horar da ma'aikatan lafiya wurin kiyayewa da dakile cututtuka masu yaduwa.

"Wasu daga cikin ma'aikatan lafiyar da suka kamu da cutar sun shiga hatsarin ne saboda rashin sanin hanyar kare kansu.

"Mun yi hanzari wurin shawo kan matsalar don bada kariya ga ma'aikatan lafiyar mu," yace.

Kamar yadda Hussaini ya bayyana, da yawa daga cikin masu cutar na cikin kananan hukumomi da ke tsakiyar birnin Kano ne.

KU KARANTA KUMA: Hasashen halin da Buhari zai shiga bayan cutar korona - Garba Shehu

A baya mun ji cewa Gwamnatin jihar Kano ta ce bidiyon filin wasa na Sani Abacha da aka mayar da shi cibiyar killacewa a kofar mota duk yunkuri ne na bata sunan ayyukan da ake.

A wata takarda da kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Malam Muhammad Garba, yace babu wata alamar gaskiya a faifan bidiyon da aka fitar.

Malam Garba yace cibiyar killacewa ta Sani Abacha, wacce aka yi don gadaje 500 an kara sauya fasalinsa tare da gyara shi daga kwamitin yaki da cutar coronavirus na fadar shugaban kasa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel