Ministar Buhari ta sadaukar da albashinta don rage cunkoson gidan gyaran hali

Ministar Buhari ta sadaukar da albashinta don rage cunkoson gidan gyaran hali

Karamar ministar babban birnin tarayya, Dr. Ramatu Aliyu, ta hakura da albashinta na watan Mayu don amfani da shi wajen biyan kudi a fitar da mutum biyar da ke gidan gyaran hali a Kuje, babban birnin tarayya.

Ministan ta sanar da wannan kyautatawar yayin shagalin bikin sallah da tayi da masu zaman gidan yarin a ranar Sallah.

Ta ce wannan kyautar za ta yi matukar amfani wajen rage cunkoson da ke gidan gyaran halin don dakile yaduwar annobar Coronavirus.

Aliyu ta tabbatar wa da mazauna gidan gyaran halin cewa za ta dauka duk matakin da ya dace a shari'ance don ganin raguwar cunkoson gidan, jaridar The Nation ta ruwaito.

Ministar Buhari ta sadaukar da albashinta don rage cunkoson gidan gyaran hali
Ministar Buhari ta sadaukar da albashinta don rage cunkoson gidan gyaran hali Hoto: The Nation
Asali: UGC

Ta ce, "Ba tallafi kadai zan yi ba, zan yi amfani da murya ta wajen rage yawan jama'ar da ke gidan nan ta hanyar belinsu.

"Zan bude hanyar kira tare da magana da manyan kasar nan saboda ba za a bar mana nauyin shugabanci nagari mu kadai ba.

"Mun san wasu daga cikinku na jiran shari'a ne, wasu kuwa an gama tasu, amma matukar akwai doka, za mu bi ta.

"Za mu yi amfani da doka wajen tabbatar da an rage cunkoson da ke gidan nan."

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin jihar Kano ta yi zazzafan martani a kan bidiyon cibiyar killacewa da ke yawo

A wani labari makamancin wannan, mun ji cewa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, ya saki fursunoni 293 da ke zaman cin sarka a wani mataki na gyara hali cikin gidajen kaso da ke fadin jihar.

An saki fursunonin masu kananan laifuka bisa ga umarnin da Gwamnatin Tarayya ta yi wa gwamnatocin jihohi na rage cunkoso a gidajen gyara hali da ke fadin kasar biyo bayan barkewara annobar cutar korona.

Kakakin Hukumar Gidajen Yari ta kasa reshen jihar Kano, DSC Musbahu Lawan Nassarawa, shi ne ya ba da tabbas a kan wannan lamari na 'yantar da fursunoni kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

DSC Lawan ya shaidawa manema labarai cewa, bayan biyan tara ta kimanin naira miliyan 12 da gwamnan ya yi, ya kuma ba wa kowane daya daga cikin fursunonin da suka shaki iskar 'yanci naira 5,000 kudin komawa gida.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel