PDP ta tabbatar da korar wasu jiga-jiganta biyu, ta dakatar da tsohon Sanata da wasu mutum 4

PDP ta tabbatar da korar wasu jiga-jiganta biyu, ta dakatar da tsohon Sanata da wasu mutum 4

- Babbar jam'iyyar adawa ta PDP reshen jihar Kaduna ta dakatar da tsohon Sanata Suleiman Hunkuyi na watanni shida cif

- An dakatar da shi ne tare da wasu mutum shida sakamakon zargin su da ake da ayyukan zagon kasa ga jam'iyyar

- Har ila yau jam'iyyar ta kori wasu 'ya'yanta biyu kwata-kwata

Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na daya daga cikin manyan jam'iyyun siyasa da ke kasar nan.

A yanzu haka babbar jam'iyyar adawar reshen jihar Kaduna ta dakatar da tsohon Sanata Suleiman Hunkuyi na watanni shida cif.

Hakazalika, Hunkuyi tsohon dan takarar kujerar gwamnan jihar ne a 2019 wanda ya sha kasa a zaben fidda gwani.

PDP ta tabbatar da korar wasu jiga-jiganta biyu, ta dakatar da tsohon Sanata da wasu mutum 4
PDP ta tabbatar da korar wasu jiga-jiganta biyu, ta dakatar da tsohon Sanata da wasu mutum 4 Hoto: First Reports
Asali: UGC

An dakatar da shi ne tare da wasu mutum shida sakamakon zargin su da ake da ayyukan zagon kasa ga jam'iyyar kamar yadda gidan talabijin din Channels ya ruwaito.

Sauran 'ya'yan jam'iyyar da aka dakatar tare da shi sun hada da Hashim Garba daga karamar hukumar Kubau, Dr Mato Dogara daga karamar hukumar Lere.

Sai kuma Ibrahim Lazuru daga karamar hukumar Lere, Dr John Danfulani daga karamar hukumar Kachia da kuma Lawal Imam Adamu daga karamar hukumar Soba.

A halin yanzu, jam'iyyar ta kori wasu 'ya'yanta biyu kwata-kwata.

Sakataren yada labarai na jam'iyyar, Abrahaman Catoh ya tabbatar da hakan a ranar Talata, 26 ga watan Mayu.

Ya ce jam'iyyar ta kori Dr John Danfulani da Ubale Salmanduna.

KU KARANTA KUMA: Shekaru 10 muka kwashe matata tana yi min fyade - Magidanci

Kamar yadda ya bayyana, korar da dakatarwa ta manyan 'ya'yan jam'iyyar ya biyo bayan hukuncin kwamitin mutum bakwai na ladabtarwa ne da aka kafa.

A wani labarin kuma mun ji cewa babbar jam’iyyar hamayya ta PDP da kungiyar gwamnoninta sun bada goyon bayansu ga tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, wanda ya na cikin manyan jiga-jiganta.

Jaridar The Guardian ta rahoto gwamnonin PDP su na cewa har gobe Sule Lamido shugaban jam’iyya ne kuma daya daga cikin jajirtattun ‘yan siyasar da ake ji da su a Najeriya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel