Malamai sun yi wa sabon shugaban ma’aikatar fadar shugaba Buhari addu’o’i

Malamai sun yi wa sabon shugaban ma’aikatar fadar shugaba Buhari addu’o’i

- Malamai sun yi wa Ibrahim Gambari addu’ar samun nasara a sabon aikinsa

- Mutanen Garin Ilorin sun shiryawa Farfesa Gambari addu’o’i na musamman

- An yi karatun Al-Kur’ani domin nemawa Hadimin Shugaban kasar sa’ar aiki

Bayan nada Ibrahim Gambari da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi a matsayin babban hadimin fadar shugaban kasa, mutanensa sun fito sun shirya masa addu’o’i a jiya.

Hukumar dillacin labarai na kasa, NAN ta ce mutanen Farfesa Ibrahim Gambari sun gudanar da taro a ranar Litinin, 25 ga watan Mayu, 2020, domin yi masa addu’ar samun sa’a.

Mutanen yankin Erubu/Asunnara/Ita Aburo a garin Ilorin, jihar Kwara ne su ka shiryawa ‘dan na su taron addu’o’i a karkashin wani babban malamin addini mai suna Uthman Erubu.

Uthman Erubu ya godewa Allah da Farfesa Ibrahim Gambari ya samu wannan mukami a fadar shugaban kasa, ya kuma roki Ubangiji ya dafa masa wajen sauke nauyin da ke kansa.

KU KARANTA: SCDDD: Farfesa Ibrahim Gambari ya ajiye tsohon aikinsa

Malamai sun yi wa sabon shugaban ma’aikatar fadar shugaba Buhari addu’o’i
Farfesa Ibrahim Gambari Hoto: Aso Rock Villa
Asali: Facebook

NAN ta ce wadanda su ka halarci wannan zama sun yi karatun Al-Kur’ani mai tsarki da nufin Ubangiji ya sa Farfesa Gambari wanda ya gaji Abba Kyari, ya yi abin kwarai a ofishinsa.

Abdulrahman Mustapha na jami’ar jihar Kwara ya yabawa irin tasirin Farfesa Gambari da aka gani a cikin al’umma, ya bayyana hadimin shugaban kasar da kwararre jakadan kwarai.

Rahotanni sun bayyana cewa, a hudubarsa, Ridwan Olagunju na sashen koyon aikin shari’a a jami’ar Ilorin, ya yi kira ga matasa su yi koyi da magabata domin gaba ta yi masu kyau.

Sarakunan gargajiya da manyan kasar Ilorin sun halarci wannan zaman addu’o’i da aka yi. An yi kira ga Gambari ya yi amfani da kwarewarsa, ya magance kalubalen da ke damun kasar.

Makonni kusan biyu kenan da Ibrahim Gambari ya zama shugaban fadar shugaban kasa. Muhammadu Buhari ya nada shi ne ya maye gurbin Abba Kyari wanda COVID-19 ta kashe.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel