Dabiri-Erewa: Jami’an tsaro su ka kori Ma’aikatan NIDCOM daga ofis

Dabiri-Erewa: Jami’an tsaro su ka kori Ma’aikatan NIDCOM daga ofis

- Ma’aikatan Hukumar NIDCOM sun ce an kore su daga ofishin da su ke aiki a Abuja

- Shugabar Hukumar kasar, Abike Dabiri-Erewa ta bayyana wannan a Ranar Asabar

- Dabiri-Erewa ta zargi ofishin Minista Isa Pantami da hannu a korar da aka yi masu

Hukumar NIDCOM mai kula da ‘yan Najeriya da ke ci-rani a kasar waje ta fito ta na kukan cewa jami’an tsaro sun kori wasu ma’aikatanta daga ofishinsu da ke babban birnin tarayya.

Shugabar hukumar NIDCOM ta kasa baki daya, Abike Dabiri-Erewa ce ta zargi jami’an tsaro da korar jami’anta daga wani ofishin da ta ke ikirarin gwamnatin tarayya ta mallaka mata.

Misis Abike Dabiri-Erewa ta bayyana haka ne da kanta a ranar Asabar, 23 ga watan Mayu, 2020, kamar yadda mu ka samu labari daga jaridar The Nation a cikin karshen wannan makon.

KU KARANTA: Karfafa shari'a da Majalisa zai hada Buhari da Gwamnoni fada

Dabiri-Erewa: Jami’an tsaro su ka kori Ma’aikatan NIDCOM daga ofis
Shugabar Hukumar da ke kula da ‘yan Najeriya da ke ci-rani a ketare
Asali: UGC

Abin da ya ba mutane mamaki shi ne NIDCOM ta ce jami’an tsaron sun yi wa ma’aikatanta wannan wulakanci ne da sa-hannun ministan sadarwa watau Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami.

“Ina birnin Addis-Ababa (kasar Habasha) lokacin da abin ya faru, aka jefa dukkanin ma’aikatana a kan titi dauke da kayan aikinmu, gafaka, da na’urorin daukar hoto duk a watse a kan titi.”

“Abin da ya fi takaici shi ne jami’an tsaron da su ka zo da makamai su ka kore mu daga ofis, sun ce su na aiki ne da umarnin ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Ali Pantami.”

A karshe shugabar ta hukumar NIDCOM ta kare jawabinta da cewa: “Na rubuta takarda na yi korafi game da wannan cin mutunci da wani bangaren gwamnati ya yi wa takwaransa.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel