Buhari: Jihohi su na banbami a kan nemawa kotu da majalisar dokoki gashin-kai

Buhari: Jihohi su na banbami a kan nemawa kotu da majalisar dokoki gashin-kai

A ranar Juma’a, 22 ga watan Mayu, 2020, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a kan dokar da ta ba majalisar dokoki da kotun jihohi damar cin gashin kansu.

Jaridar The Nation ta ce gwamnonin jihohi da-dama sun girgiza da wannan mataki da shugaban kasar ya dauka, ganin cewa su na tsakiyar tattaunawa da shugaban a kan wannan batu.

Rahotannin jaridar sun bayyana cewa akwai gwamnoni da ke duba yiwuwar shiga kotu da gwamnatin tarayya a game da lamarin. Jihohin su na ganin an daba masu wuka a zuciya.

Amma kuma a wani bangare, manyan lauyoyi sun yabawa shugaba Muhammadu Buhari a kan wannan matsaya. Daga ciki har da irinsu fitaccen lauyan nan na kasa watau Femi Falana.

Marigayi Abba Kyari ne ya fara aikin yadda za a ba majalisar dokokin jihohi da bangaren shari’a gashin kansu. Shugaban ma’aikatar fadar shugaban kasar ya mutu kafin a karkare aikin.

KU KARANTA: Yarjejeniyar Buhari da Gwamnoni a kan batun sallar Idi

Buhari: Jihohi su na banbami a kan nemawa kotu da majalisar dokoki gashin-kai
Buhari ya na sa hannu a takarda Hoto: Pulse NG
Asali: Twitter

Gwamnonin su na ikirarin gaggawar da shugaban kasar ya yi wajen sa hannu a wannan doka, ya rusa zaman da kungiyar gwamnoni ta NGF ta ke yi da shugabannin majalisu na jihohi.

NGF da majalisar dokokin su na kokarin kawo yadda za su shawo kan yadda za a ba ‘yan majalisa damar cin gashin kansu, sai kwatsam annobar COVID-19 ta sa maganar ta su ta tsaya cak.

Wani gwamnan jam’iyyar PDP ya shaidawa jaridar cewa: “Mun yi mamakin jin matakin da shugaban kasa ya dauka, wannan doka ta fi kama da ta mulkin soja ba damukaradiyya ba.”

“Dokar ba za ta tsayu ba, za mu kalubalance ta a kotu. Jam’iyyarmu ba ta goyon bayan hana majalisa da bangaren shari’a gashin kansu, amma sai an yi wa tsarin mulki kwaskwarima.”

“Ana yunkurin komawa mulkin soja da wadannan dokoki da shugaban kasa ya ke rattabawa hannu. Ba za mu bari a sabawa kundin tsarin mulkin 1999 ba.” A cewar gwamnan adawan.

Wani gwamna ya ce: “Abin da ba mu taba tunani ba ne, wuce gona da iri ne, kuma sabawa zaman da gwamnoni su ke yi da Buhari ne.” Wasu kuma su na ganin an shiga hurumin majalisa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng