Yan sanda sun kashe masu garkuwa da mutane 8 da aka dade ana nema

Yan sanda sun kashe masu garkuwa da mutane 8 da aka dade ana nema

- Rundunar 'yan sandan jihar Taraba ta halaka wasu 'yan bindiga takwas da suka dade suna damun jihar

- 'Yan bindigar sun addabi jama'ar da ke karamar hukumar Bali ta jihar ta yadda suke garkuwa da mutane tare da karbar kudin fansa

- Kakakin rundunar 'yan sandan jihar ya ja kunnen 'yan ta'addan da ke yankin da su mika kansu ko kuma su fuskanci fushin hukuma

Rundunar 'yan sandan jihar Taraba ta kashe wasu fitinannun 'yan bindiga takwas da suka dade suna gallabar yankin kuma ake ta nemansu tun watannin da suka gabata.

An kashe 'yan bindigar ne a karamar hukumar Bali ta jihar bayan bayanan sirrin da aka samu a kan maboyarsu.

Sun kware a yin garkuwa da jama'ar yankin tare da karbar kudin fansa, gidan talabijin din Channels ya ruwaito.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, David Misal ne ya sanar da hakan bayan ya ga gawawwakin masu garkuwa da mutanen a ranar Juma'a.

Kamar yadda Misal ya tabbatar, bayan 'yan bindiga sun hango jami'an tsaron sai suka bude musu wuta tare da musayar harsasai.

Hakan ne ya yi sanadiyyar mutuwarsu kuma an samo harsasai, bindigogin da kuma kayan sojoji.

Misal ya ja kunnen duk wani dan ta'adda a yankin da ya tuba ko kuma ya mika kanshi, idan ba haka ba zai fuskanci fushin hukumar.

Yan sanda sun kashe masu garkuwa da mutane 8 da aka dade ana nema
Yan sanda sun kashe masu garkuwa da mutane 8 da aka dade ana nema. Hoto daga HumAngle
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Ba a ga wata ba a Najeriya, Idi sai ranar Lahadi –Sarkin Musulmi

A wani labari na daban, majalisar Koli ta harkokin addinin musulunci ta Najeriya, NSCIA, ta sanar cewa za a cigaba da azumi a ranar Asabar.

Kwamitin duban wata ta NSCIA ta ce ba a ga wata ba a kasar saboda haka za a cigaba da azumi a ranar Jumaa.

Ta ce za a gudanar da azumi talatin a bana ba kamar yadda wasu musulmi suka fara shirin yin Idi a ranar Asabar ba.

Da ta ke sanar da sakamakon neman watar a ranar Jumaa, ta sanar da cewa "Ba a ga jaririyar watar Shawwal ba a Najeriya, gobe 30 ga watan Ramadan. Za a fitar da sanarwar daga ofishin sarkin musulmi nan ba da dadewa ba."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164