Zaben gwamnan Ondo da Edo: Tsohon shugaban APC ya fallasa yan takarar da Buhari ke goyon baya

Zaben gwamnan Ondo da Edo: Tsohon shugaban APC ya fallasa yan takarar da Buhari ke goyon baya

Tsohon shugaban APC ta kasa, John Odigie Oyegun ya bayyana shugaban kasa Muhammadu Buhari na goyon bayan Rotimi Akeredolu da Godwin Obaseki don zarcewa a mukamansu.

Rotimi Akeredolu ne gwamnan Ondo, yayin da Godwin Obaseki ne gwamnan Edo, dukkanin zasu kammala wa’adinsu na farko nan bada jimawa, don haka suke neman zarcewa a mulki.

KU KARANTA: Annobar Corona: Babu makawa sai tattalin arzikin Najeriya ya tabarbare – Ministar kudi

A nata bangaren, hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, ta sanya ranar 19 ga watan Satumba don gudanar da zaben jahar Edo, yayin da ta sanya 10 ga watan Oktoba don zaben Ondo.

Cikin wani talla da aka watsa a wasu zababbun jaridun kasar, an ruwaito Oyegun yana fadin shugaba Buhari ya gamsu da salon kamun ludayin game da sha’anin mulki a jahohinsu.

Zaben gwamnan Ondo da Edo: Tsohon shugaban APC ya fallasa yan takarar da Buhari ke goyon baya
Obaseki/Akeredolu Hoto: TheCable
Asali: UGC

Don haka Oyegun yace shugaban kasa Muhammadu Buhari na ganin kamata ya yi a basu daman tsayawa takara karo na biyu, sai dai kuma idan su ne basu da muradi.

“Na yi maraba da labarin da na samu na cea shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da yarjejeniyar da aka cimmawa don shawo kan rikicin shugabanci da ya dabaibaye jam’iyyar APC.

“Daga cikin yarjejeniyar akwai cewa gwamnonin Edo da Ondo, Godwin Nogheghase Obaseki da Oluwarotimi Akeredolu sun yi rawar gani a jahohinsu, don haka a basu daman sake tsayawa takara sai dai idan basu so.

“Ma’ana jam’iyyar ta dinke barakarta da goya ma gwamnonin baya, don haka bai kamata a bari shuwagabannin jam’iyyun a jahohin biyu su gudanar da zabukan fidda gwani ba, dole ne a bi ka’ida wajen gudanar da zabukan.” Inji shi.

Oyegun na da kyakkyawar alaka da gwamnonin biyu sakamakon a zamaninsa ne suka lashe zabukan gwamnonin jahohinsu, tare da gudunmuwarsa da ta uwar jam’iyyar APC.

A wani labari, bincike na tsimi da tanadi da hukumar kiddiga ta Najeriya ta gudanar ya nuna tattalin arzikin Najeriya zai shiga halin tabarbarewa da kashi -4.4 saboda annobar Coronavirus.

Premium Times ta ruwaito ministar kudi, Zainab Ahmad ce ta bayyana haka ga manema labaru bayan kammala taron majalisar tattalin arzikin kasa daya gudana a ranar Alhamis.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel