Dino: Ba ni da niyyar sa motoci na a kasuwa, kudin wasu ma na ke nema

Dino: Ba ni da niyyar sa motoci na a kasuwa, kudin wasu ma na ke nema

Fitaccen ‘dan siyasar nan, Dino Melaye ya maida martani ga abokan adawa da masu sukarsa a dalilin yadda ya ke yi wa Duniya tallar arzikin tarin dirka-dirka motocinsa.

A kwanan bayan nan wasu su ka fito su na kira ga Dino Maleya ya saida motocin da ya mallaka. ‘Dan siyasar ya fitar da wani bidiyo, inda ya ce ba zai biyewa masu wannan kira ba.

Sanatan ya fitar da wani bidiyo ne a ranar Litinin, ya na mai magana ga wadanda su ka huro masa wuta, ya ce sai a dauka saida motocinsa zai kawo karshen matsalolin kasar.

A wannan bidiyo, ‘dan siyasar adawar ya bayyana cewa bai taba ikirarin shi mutum ne wanda ya cika goma ba, ya ce duk da haka ya na bakin kokari na ganin ya taimaki mutanensa.

Sanata Dino Melaye ya fito ya na cewa: “Gaskiyar magana ita ce, idan har na saida duk abubuwan da na mallaka, to zan tsiyace. Kuma attajirai ne kadai za su iya taimakon talakawa.”

KU KARANTA: Dino Melaye ya fadi abin da zai yi maganin cutar COVID-19

Dino Melaye ya nuna cewa idan har ya tsiyace, babu shakka ba zai samu damar taimakon marasa hali ba. Melaye ya kara da cewa: “Matsiyaci ba zai iya taimakon matsiyaci ba.”

Tsohon sanatan na Kogi ta yamma ya ce shi ba mutum ba ne da ya ke sakin hannunsa ba tare da ya yi tunani ba, ya ce ya na yin kyauta ne bisa umarnin da Ubangiji ya yi masa.

A cewar Melaye, kowa ya na da abin da ya ke sha’awa, wasu su na sha’awar wayoyin salula ne, shi kuwa motoci ne su ke burgesa, kuma burinsa shi ne ya ma karo wasu motocin.

Da ya ke jawabi a wannan bidiyo da yanzu ya baza gari, Melaye ya ce ya bada sautun wasu motocin wanda yanzu su na tafe ta ruwa. Hakan na nufin motocin sun kusa isowa.

“Ba zan saida wata motata ba, ina addu’a ne ma Ubangiji ya kara mani dukiya in saye wasu. Abin da na ke sha’awa shi ne motoci, yanzu haka ina jiran wasu motocin ne su karaso."

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel