Edo da Ondo: APC ta fitar da farashin fom din takarar gwamna da na mataimaki
Jam'iyyar APC mai mulki ta ce ma su son yin takarar gwamna a zaben da za a yi ranar 19 ga watan Satumba da 10 ga watan Oktoba a jihohin Edo da Ondo za su biya miliyan N22.5 a matsayin kudin fom din takara.
A cikin sanarwar da sakataren tsare - tsaren APC, Emma Ibediro, ya fitar a Abuja ranar Laraba, jam'iyyar ta ce za ta fara sayar da fom ga ma su sha'awar takara gabanin gudanar da zaben cikin gida na fidda dan takara.
A cewar Ibediro, jam'iyyar APC za ta fara sayar da fom din takarar gwamna a jihar Edo daga ranar 20 ga watan Mayu zuwa ranar 2 ga watan Yuni, yayin da za ta fara sayar da na takarar gwamna a jihar Ondo daga ranar 11 ga watan Yuni zuwa ranar 1 ga watan Yuli.
A cikin watan Fabrairu ne hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta tsayar da ranar 19 ga watan Satumba da ranar 10 ga watan Oktoba a matsayin ranakun gudanar zabe a jihohin Edo da Ondo.
Sakatarn tsare - tsaren ya ce za a sayar da fom din takarar gwamna a kan N22.5m a dukkan jihohin, ba tare da banbanci a farashin ba.
A cewarsa, kudin sun hada da miliyan N2.5 kudin nuna sha'awar takara da miliyan N20 kudin fom din takara.
DUBA WANNAN: 'Kar ka bari a yi Sallar Idi a Kaduna' - Sheikh Gumi ya shawarci El-Rufa'i
"Babu banbancin farashi a tsakanin fom din takarar gwamna da na mataimaki.
"Mata da ma su bukata ta musamman da ke sha'awar yin takara za su biya kaso 50 na adadin kudin," a cewar sanarwar.
Mista Ibediro ya ce za a biya kudin fom din a asusun bankin uwar jam'iyya.
Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa jam'iyyar APC za ta gudanar da zaben fidda dan takarar kujerar gwamnan jihar Edo a ranar 22 ga watan Yuni, yayin da za ta yi na jihar Ondo a ranar 20 ga watan Yuli.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng