Sallar Idi: Zulum ya umarci limamai da kwamitin yaki da COVID-19 su tattauna

Sallar Idi: Zulum ya umarci limamai da kwamitin yaki da COVID-19 su tattauna

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bai wa shugaban kwamitin yaki da cutar korona ta jihar, Umar Kadafur, umarni tuntubar Shehun Borno tare da yin taro da malamai da limaman jihar a kan sallar Idi a fadin jihar.

Mataimaki na musamman ga gwamnan a kan hulda da jama’a, Malam Isa Gusau ne ya sanar da hakan a wata takarda da ya fita a ranar Laraba da safe.

“Babu shakka cutar korona na da matukar hatsari don haka dole a dauki matakan kiyaye yaduwarta. A don haka, dole ne mu hada kai wajen sauke nauyin da ya hau kanmu na yaki da annobar ballantana a bangarorin da ya shafi addini.

“A shekarun da suka gabata, jihar Borno ta shiga tsaka mai wuya. Mun san lokutan da ‘yan jihar ke take dokar gwamnati don takawa zuwa filin sallar idi. Amma kuma a kan samu akasi inda kungiyar yan ta'adda ke kai musu hari.

“Wannan makamancin abu ne, tunda duk fata a ke yi kada a rasa rayuka. Dole ne a duba ra’ayin ‘yan kasa tare da kuma duban fannin addinai ba tare da an watsar da gwamnati ba.

“Za mu mayar da hankali wajen duba tare da sauke nauyin jama’ar jihar ba tare da an yi watsi da abinda ya dace ba,” Zulum yace.

Sallar Idi: Zulum ya umarci limamai da kwamitin yaki da COVID-19 su tattauna
Sallar Idi: Zulum ya umarci limamai da kwamitin yaki da COVID-19 su tattauna Hoto: The Governor of Borno State
Asali: Facebook

Ya kara da cewa, “A don haka ne nake umartar shugaban kwamitin yaki da cutar korona ta jihar Borno da ya tuntubi mai martaba Shehun Borno tare da yin taron malamai da limami don samun matsaya.

“Ba hana yaduwar cutar korona kadai za a duba ba yayin yanke hukunci, a duba yadda za a dakile dukkan harin ‘yan ta’adda. A tattauna a kan yadda za a yi amfani da takunkumin fuska, wanke hannaye da sauransu.

“A kara samar da filayen sallar da za su kasance babu cunkoso kuma za a iya kiyaye dokar nesa-nesa da juna.”

Gwamnan ya kara da cewa, ba zai yi kasa a guiwa ba wajen rungumar duk abinda suka tattauna a kai tare da yin aiki da shi koda kuwa ba irin shi ne a zuciyarsa ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel