El-Rufai ya bada umarnin sakin albashin watan Mayu na ma'aikatan jihar

El-Rufai ya bada umarnin sakin albashin watan Mayu na ma'aikatan jihar

Gwamnatin jihar Kaduna ta bai wa ma'aikatar kudi ta jihar umarnin biyan albashin watan Mayun 2020 a ranar Talata, kwanaki shida kafin ranar biyan albashin ma'aikatan.

Kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta bayyana, mataimakiyar gwamnan, Dr Hadiza Balarabe, ta bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a gidan gwamnati na Sir Kashim Ibrahim a ranar Talata.

A wata takarda da mai bai wa gwamnan shawara ta musamman a fannin yada labarai, Muyiwa Adekeye ya fitar, mataimakiyar gwamnan ta ce wannan kyautatawar ta biyo bayan kokarin gwamnatin na ganin ma'aikatan sun yi amfani da ranakun Laraba da Alhamis don siyayyar sallah.

El-Rufai ya bada umarnin sakin albashin watan Mayu na ma'aikatan jihar

El-Rufai ya bada umarnin sakin albashin watan Mayu na ma'aikatan jihar Hoto: Daily Nigerian
Source: Facebook

Idan za mu tuna, gwamnatin jihar ta bayyana wasu ranaku da mazauna jihar za su nemi ababen amfani don shagalin bikin sallah.

Mataimakiyar gwamnan ta shawarci ma'aikatan gwamnatin jihar da su yi amfani da abubuwan da suka samu don matsanancin lokacin da ke karatowa.

"Gwamnatin jihar Kaduna cewa ta farko da ta fara biyan sabon mafi karancin albashi wanda aka daidaita a watan Satumban 2019.

"Gwamnatin jihar ta kaddamar da karancin albashinta kafin gwamnatin tarayya ta kammala tattaunawa," Balarabe tace.

KU KARANTA KUMA: Bude masallatai: Majalisar malaman Kano ta yi zazzafan martani ga Ganduje

A baya mun ji cewa gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya yi wa malaman da suka zargesa da hana sallar Juma'a a jihar 'Allah ya isa'.

Gwamnan ya ce ya bar malaman da Allah ne a jawabin da ya yi ga 'yan jiharsa a yammacin Talata.

Gwamnan ya tabbatar da cewa ba zai bar kowanne mutum shiga jihar Kaduna a ranar Sallah daga Kano ba. Kasancewar gwamnatin jihar Kano ta amince da gudanar da sallar Idi da Juma'a.

Ba kamar wasu jihohi ba, El-Rufai ya ce kowa yayi sallar idi da Juma'a a gida don dakile yaduwar cutar korona da ke yi wa duniya barazana.

Har ila yau, gwamnan ya zargi jami'an tsaro da cin amana inda ya ce suna karbar na goro domin barin jama'a su shiga jihar Kaduna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel