Boko Haram: An yi wa Sojoji 9 rauni, an kashe ‘Yan ta’adda 20 a Baga

Boko Haram: An yi wa Sojoji 9 rauni, an kashe ‘Yan ta’adda 20 a Baga

- An yi wata gwabzawa tsakanin Sojoji da Boko Haram a Garin Baga

- A sanadiyyar wannan karo, an yi raga-raga da ‘Yan ta’adda har 20

- John Enenche ya sanar da wannan a wani jawabi da ya fitar a jiya

A ranar Lahadin da ta gabata, dakarun sojojin Najeriya su ka kashe ‘yan ta’addan Boko Haram wadanda yanzu ake kira ISWAP. An hallaka ‘yan ta’addan ne a Bama, a jihar Borno.

Wani babban jami’in sojojin kasa da ke da alhakin yada labarai, John Enenche ya bayyana wannan washe garin wannan fafafatawa. Ya bayyana haka ne a jawabin da ya fitar.

An yi wa wasu sojoji tara rauni a sakamakon wannan arangama, inda mayakan su ka nuna kwarewarsu wajen harbin bindiga. An kuma yi nasarar karbe makaman ‘yan ta’addan.

Daga cikin makaman da aka karbe daga hannun Boko Haram akwai bindigogin AK-47 shida, casbi 520 na harsashi mai tsawon 7.62 da manyan makamai da kananan bama-bamai.

KU KARANTA: Mayakan ISWAP da Sojojin kasa su ka hallaka a Arewa maso Gabas

Gidan sojan ta ce wadannan ‘yan ta’adda su na shirin kai hari ne a garin Baga, sai labari ya zo masu. A karshe sojojin kasar sun yi galaba a kan mayakan inda su ka hallaka wasunsu.

“Sai dai sojojinmu tara sun samu rauni a wurin fadan, amma babu wanda aka rasa. An tafi da wadanda aka yi wa rauni zuwa asibitin Bataliya ta uku domin a duba su.” Inji Enenche.

A karshen jawabin, Enenche ya ce “Laftana Janar Tukur Buratai ya yabawa kokarin sojojin da su ka nuna kwarewa, ya bukaci su tsaya tsayin-daka wajen ganin bayan ‘yan ta’adda.”

Kwanakin nan Janar Tukur Buratai da sauran shugabannin hafsun soji da 'yan sanda su kaga gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a game da lamarin tsaro a fadin kasar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel