Sojojin bogi da su ka kashe kurtun dan sanda sun shiga hannu

Sojojin bogi da su ka kashe kurtun dan sanda sun shiga hannu

'Yan sanda a jihar Legas sun kama wasu sojojin bogi biyu; Kehinde Elijah, mai shekaru 45, da Eze Joseph, bisa zarginsu da hannun a kisan kurtun dan sanda, Onalaja Onajide, mai mukamin saja.

Sojojin bogin sun harbe Onajide da misalin karfe 9:30 na daren ranar 10 ga watan Mayu a gaban babban ofishin 'yan sanda na Ilemba Hausa Division da ke Ajamgbadi a garin Legas.

Wata tawagar 'yan sanda a karakshin jagorancin CSP Yahaya Adesina, DPO na ofishin Ilemba Hausa Division, ta samu nasarar kama sojojin bogin da su ka harbe saja Onajide. An kama su ne ranar Asabar, 16 ga watan Mayu.

Bincike ya nuna cewa daya daga cikin sojojin bogin, Elijah, tsohon soja ne da aka kora daga aiki bayan ya gudu daga yankin arewa maso gabas, inda sojoji ke yaki da 'yan ta'addar kungiyar Boko Haram.

Korarren sojan na yawan ziyartar ofishin 'yan sanda na Ilemba Hausa a cikin basajan shi soja ne a rundunar soji ta Najeriya.

Sojojin bogi da su ka kashe kurtun dan sanda sun shiga hannu

Sojojin bogi da su ka kashe kurtun dan sanda
Source: UGC

Elijah ya gayyato wasu mutane da suka zo cikin kakin sojoji a cikin wata karamar mota kirar 'Lexus' saboda jami'an 'yan sandan ofishin sun kama motarsa a ranar.

DUBA WANNAN: An raunata mutane 8 yayin rikici tsakanin 'yan Izala da Tijjaniyya a kan limancin Masallacin Juma'a

A yayin da jami'an 'yan sanda ke tuhumarsa, Elijah ya bayyana cewa ya gudu daga rundunar soji da bindigarsa da kaki da sauran kayan aikin sojoji.

A yayin da 'yan sanda ke gudanar da bincike, sun gano cewa an aikata laifin kisan da Joseph, mazaunin yankin Ajangbadi, wanda aka samu karin kakin soji guda uku a gidansa.

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Legas, Bala Elkana, ya ce wasu batagari ne su ka harbe marigayi Onajide.

"Wasu 'yan iskan gari ne su ka harbe shi. Mu na tsare da wadanda ake zargi da aikata kisan, a yayin da mu ke cigaba da bincike," a cewar Elkana.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel