Ganduje ya zabge kaso 50 na albashinsa da sauran ma su rike da mukaman siyasa a Kano

Ganduje ya zabge kaso 50 na albashinsa da sauran ma su rike da mukaman siyasa a Kano

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya zabge kaso hamsin a albashin dukkan ma su rike da mukaman siyasa da ya nada da wadanda aka zaba a fadin jihar Kano.

Hakan na kunshe ne a cikin wani jawabi da babban mai taimakawa Ganduje a bangaren yada labarai, Abubakar Aminu, ya fitar ranar Lahadi.

A cikin jawabin, an rawaito gwamna Ganduje na cewa rage albashin ya biyo bayan raguwar da aka samu a kudaden shiga da kasa ke samu saboda kalubalen annobar cutar korona.

Ya bayyana cewa ragin albashin zai fara aiki daga wannan watan na Mayu da mu ke ciki.

"Faduwar farashin man fetur a kasuwar duniya ya shafi tattalin arzikin duniya, hakan ya jawo raguwar kudaden da tarayya ke bawa jihohi, a saboda haka jihar Kano ta zabge albashin dukkan ma su rike da mukaman siyasa da kaso hamsin.

"Ragin albashin ya shafi gwamna, mataimakinsa, kwamishinoni, mataimaka na musamman, ma su bayar da shawara da sauransu.

"A matakin kananan hukumomi, ragin ya shafi shugabannin kananan hukumomi, mataimakansu, zababbun kansiloli, sakatarori da ma su bayar da shawara.

"An samu gagarumin ragi a kudaden shiga da jiha ke samu a cikin gida saboda kalubalen annobar korona, kusan dukkan kamfanoninmu yanzu a rufe su ke, ba sa aiki," kamar yadda jawabin ya kunsa.

Ganduje ya zabge kaso 50 na albashinsa da sauran ma su rike da mukaman siyasa a Kano

Ganduje
Source: UGC

Da yammacin ranar Lahadi ne Legit.ng ta wallafa rahoton cewa gwamnatin tarayya (FG) ta damka tallafin kayan abinci a tirela fiye da 120 ga gwamnatin jihar Kano.

DUBA WANNAN: Buhari ya rasa farin jininsa a wurin talaka, ba zai ci zabe ba da zai sake tsayawa takara - Jigo a APC, Dan Bilki Kwamnada

Tallafin na daga cikin kokarin gwamnati na ragewa jama'a radadi da matsin da suka shiga sakamakon bullar annobar korona.

Hakan na kunshe ne a cikin wani takaitaccen sako da hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad, ya fitar a shafinsa na tuwita da yammacin ranar Lahadi.

Ministar walwala, jin kai da bayar da tallafi, Sadiya Umar Farouk, ta damka tallafin kayan abincin ga gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

Sanarwar ba ta bayyana lokaci ko a wurin da aka damka tallafin ga gwamnatin Kano ba.

Kazalika, gwamnatin Kano ba ta fitar da sanarwa a kan bayar da tallafin ba har ya zuwa wannan lokaci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel