Malaman Kaduna sun roki Nasir El-Rufai ya sassauta takunkumin kulle
Majalisar limamai da malaman addinin musulunci na jihar Kaduna, sun fara kira ga gwamnati ta cire dokar zaman gidan da ta kakabawa jama’a a sanadiyyar annobar Coronavirus.
Jaridar Daily Trust ta ce shugaban majalisar limamai na Kaduna, Shaykh Ibrahim Nakaka ne ya yi wannan roko a wani jawabi da ya fitar dazu a ranar Lahadi, 17 ga watan Mayu, 2020.
Shaykh Ibrahim Nakaka ya yabawa gwamnatin Malam Nasir El-Rufai game da irin matakan da ta yi maza ta dauka domin yaki da annobar cutar COVID-19 da hana cutar yaduwa a jihar.
“Majalisar limamai ta yabawa kokarin da gwamna Mallam Nasiru Ahmad El-Rufai da mataimakiyarsa, Dr Hadiza Balarabe ta yi a lokacin da mai girma gwamna ba ya nan.”
“Balarabe ta yi kokarin hana Coronavirus barkewa a Kaduna, idan aka kwatanta da sauran jihohin da ake makwabtaka da su da su ka gaza daukar mataki da wuri.” inji Shaykh Nakaka.
KU KARANTA: PDP ta dakatar da Sule Hunkuyi, Danfulani da wasu Jiga-jigai a Kaduna
“Majalisar ta na ganin cewa lokaci ya yi da za a sassautawa jama’a wahalar da su ka shiga a jihar Kaduna, a daidai wannan lokaci kuma ka da ayi wasa da yakin da ake yi da Coronavirus.”
Shehin ya ce: “Saboda nasarorin da aka samu, majalisar ta na kira ga gwamnatin jiha ta fara neman hanyar sassauta takunkumin sannu a hankali, amma a kafa tsauraran matakai.”
Ibrahim Nakaka ya ce “A cigaba da amfani da kariyar fuska, a kara kokari wajen wayar da kan jama’a a game da yaki da cutar, sannan a rika amfani da sabulu da man wanke hannu.”
A cewar Nakaka, ko da za a cire dokar zaman gida, ka da a bude iyakokin jihar. Malamin ya ce gwamnati ta dakata da sakin hanyoyi shigowa Kaduna har sai an tsira daga COVID-19.
Jaridar Daily Trust ta ce majalisar ta yi kira ga musulmai su tsaya tsayin-daka da addu’o’i a wannan wata mai alfarma na Ramadan domin Ubangiji ya yi maganin cutar Coronavirus.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng