An kama wasu yaran kasurgumin dan ta'adda 'Gana', an kama mambobin kungiyar Bassa yayin da suke shirin kai hari a Nasarawa

An kama wasu yaran kasurgumin dan ta'adda 'Gana', an kama mambobin kungiyar Bassa yayin da suke shirin kai hari a Nasarawa

Dakarun rundunar sojin Najeriya a karkashin atisayen 'Whirl Stroke' sun samu nasarar cafke wasu hatsabiban 'yan ta'adda da ke da nasaba da kasurgumin dan ta'addan nan na jihar Benuwe mai suna 'Gana'.

A cikin sanarwar da rundunar soji ta wallafa a shafinta na tuwita, ta bayyana cewa ta samu nasarar kama wasu mambobin kungiyar 'yan ta'adda mai suna 'Bassa'.

An kama su ne a yankin karamar hukumar Doma ta jihar Nasarawa yayin da suke kokarin kai hari a kan wasu kauyukan Tiv.

Rundunar soji ta ce sun shiga hannu ne bayan samun sahihan bayanan sirri a kan shirin da suke yi na kai harin a kan 'yan kabilar Tiv da suke rikicin iyaka da su.

Sojoji sun kwace muggan makamai daga hannun 'yan ta'addar, kamar yadda suka nuna a cikin faifan bidiyo.

An kama wasu yaran kasurgumin dan ta'adda 'Gana' yayin da suke shirin kai hari a Nasarawa
An kama wasu yaran kasurgumin dan ta'adda 'Gana' yayin da suke shirin kai hari a Nasarawa
Asali: Twitter

An kama wasu yaran kasurgumin dan ta'adda 'Gana' yayin da suke shirin kai hari a Nasarawa
An kama wasu yaran kasurgumin dan ta'adda 'Gana' yayin da suke shirin kai hari a Nasarawa
Asali: Twitter

An kama wasu yaran kasurgumin dan ta'adda 'Gana' yayin da suke shirin kai hari a Nasarawa
An kama wasu yaran kasurgumin dan ta'adda 'Gana' yayin da suke shirin kai hari a Nasarawa
Asali: Twitter

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, mayakan kungiyar Boko Haram sun kai hari sansanin bataliyar dakarun sojin Najeriya ta 156 da ke yankin Mainok a jihar Borno, tare da kashe sojoji biyar.

Jaridar Punch ta ce wani rahoto da ta samu daga dakin watsa labaran rundunar soji ya nuna cewa mayakan kungiyar sun kai harin ne a cikin motocin yaki da yawansu ba zai gaza goma ba.

Rahoton, wanda ya fito daga hedikwatar rundunar ofireshon Lafiya Dole ya bayyana cewa mayakan sun fuskanci tirjiya tare da mayar da martani daga dakarun soji, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwa da dama daga cikinsu.

"Karin bayani dangane da harin da aka kai kan bataliyar soji ta 156 da ke Mainok; mayakan Boko Haram sun kai hari bataliyar soji ta 156 da ke garin Mainok da motocin yaki a kalla 10.

"Sun fara kai hari garin Mainok kafin daga bisani su kai hari sansanin sojoji. Dakarun soji sun mayar da martani nan take.

"Sojoji sun samu gudunmawa daga hedikwatar soji ta 29 a karkashin jagorancin birgediya janar O. G. Onubogu. Amma, mayakan Boko Haram da suka fuskanci tirjiya daga sansanin soji na Mainok, sun kai wa tawagar Onubogu harin kwanton bauna a kan hanyarsu ta zuwa Mainok.

"Tawagar sojojin ta fuskanci mayakan da karfin makaman da suke da su, kuma sun karasa sansanin soji na 156 bayan mayakan Boko Haram sun ji azaba, sun gudu saboda an fi karfinsu.

DUBA WANNAN: Gwamnati ta gano biliyan N4.3 da aka boye tsawon shekaru 10 a wani asusun sirri

"Ba mu tabbatar da adadin makiyan da dakarun soji su ka kashe ba, amma an zubar da jini a kewayen sansanin da aka yi bata kashi.

"Sojoji biyu daga cikin dakarun sansanin bataliya ta 156 sun rasa ransu, yayin da uku daga cikin tawagar da aka kaiwa harin kwanton bauna suka rasa ransu. Yanzu komai ya daidaita a Mainok, babu sauran wani tarnaki," a cewar rahoton.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng