Buhari ya yi wa Garba ta’aziyyar mutuwar Mahaifinta wanda ya yi masa direba

Buhari ya yi wa Garba ta’aziyyar mutuwar Mahaifinta wanda ya yi masa direba

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya rasa wani tsohon direbansa a lokacin da ya ke gidan soja. Buhari ya yi aiki a gidan soja na tsawon shekara 24 kafin ya yi ritaya.

Kofral Garba Tizhe Tumba mai ritaya ya rasu ne bayan ya yi fama da wata gajerar rashin lafiya a wani kauye Bazza, a karamar hukumar Michika, da ke cikin jihar Adamawa.

Garba Tizhe Tumba shi ne mahaifin tsohuwar sanatar APC ta yankin Adamawa ta Arewa watau Misis Binta Masi Garba, wanda fitacciyar ‘yar siyasa ce a Arewacin Najeriya.

Marigayin ya kasance direban Muhammadu Buhari, wanda shugaban kasar ya yi wa addu’a karshen makon nan ta bakin mai magana da yawunsa watau Garba Shehu.

Shugaban na Najeriya ya bayyana Garba Tizhe Tumba a matsayin mutum mai kishi da rikon amana, kuma wanda ya san darajar aiki, har ila yau ya kira shi soja mai daraja.

KU KARANTA: NCDC: COVID-19 ta sake harbin mutane fiye da 170 a Najeriya

A jawabin, shugaban kasa Buhari, ya yi wa tsohon sojan addu’ar Ubangiji ya yi masa rahama, sannan kuma ya yi wa iyalinsa ta’aziyyar wannnan babban rashi da aka yi.

Jaridar Daily Trust ta ce mai taimakawa shugaban kasar wajen yada labarai ya fitar da wannan jawabi ne a madain Muhammadu Buhari a ranar 16 ga watan Mayu, 2020.

‘Diyar marigayin, Binta Masi Garba ta taba wakiltar yankin Kaduna ta kudu a majalisar wakilai, daga baya ta koma jiharta Adamawa ta zama ‘yar majalisar dattawa a APC.

Idan ba za ku manta ba kwanakin baya wani tsohon mai gadin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rasu. Lawal Mato ya cika ne bayan rasuwar Abba Kyari a watan jiya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel