Masari ya sassauta dokar kulle jihar Katsina
Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya bayar da umarnin sassauta dokar kulle jihar Katsina na tsawon mako guda.
Sakataren gwamnatin jihar Katsina (SSG), Mustapha Inuwa, ne ya sanar da hakan a cikin wani jawabi da ya fitar ranar Asabar.
Ya bayyana cewa gwamnati ta yanke shawarar sassauta dokar ne bayan ganawarta da shugabannin addini da sauran masu ruwa da tsaki a jihar yayin taron da ta saba gudanarwa.
Inuwa ya bayyana cewa sassauta dokar kullen za ta fara aiki ne daga ranar Litinin, 18 ga watan Mayu, zuwa ranar Lahadi, 24 ga watan Mayu.
Ya ce za a sassauta dokar ne a cikin kananan hukumomin jihar, amma kuma dokar hana bulaguro zuwa wasu kananan hukumomin ta na nan daram.
Ya bayyana cewa gwamna Masari ya umarci sarkin Daura da na Katsina da sauran manyan masu rike da sarautar gargajiya a kan su tabbatar da cewa dagatai sun zauna a garuruwansu tare da jama'arsu yayin bukukuwan Sallah.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng