Mayakan Boko Haram sun kai hari sansanin sojoji da motocin yaki 10, sun kashe dakaru 5

Mayakan Boko Haram sun kai hari sansanin sojoji da motocin yaki 10, sun kashe dakaru 5

Mayakan kungiyar Boko Haram sun kai hari sansanin bataliyar dakarun sojin Najeriya ta 156 da ke yankin Mainok a jihar Borno, tare da kashe sojoji biyar.

Jaridar Punch ta ce wani rahoto da ta samu daga dakin watsa labaran rundunar soji ya nuna cewa mayakan kungiyar sun kai harin ne a cikin motocin yaki da yawansu ba zai gaza goma ba.

Rahoton, wanda ya fito daga hedikwatar rundunar ofireshon Lafiya Dole ya bayyana cewa mayakan sun fuskanci tirjiya tare da mayar da martani daga dakarun soji, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwa da dama daga cikinsu.

"Karin bayani dangane da harin da aka kai kan bataliyar soji ta 156 da ke Mainok; mayakan Boko Haram sun kai hari bataliyar soji ta 156 da ke garin Mainok da motocin yaki a kalla 10.

"Sun fara kai hari garin Mainok kafin daga bisani su kai hari sansanin sojoji. Dakarun soji sun mayar da martani nan take.

"Sojoji sun samu gudunmawa daga hedikwatar soji ta 29 a karkashin jagorancin birgediya janar O. G. Onubogu. Amma, mayakan Boko Haram da suka fuskanci tirjiya daga sansanin soji na Mainok, sun kai wa tawagar Onubogu harin kwanton bauna a kan hanyarsu ta zuwa Mainok.

Mayakan Boko Haram sun kai hari sansanin sojoji da motocin yaki 10, sun kashe dakaru 5
Mayakan Boko Haram sun kai hari sansanin sojoji da motocin yaki 10, sun kashe dakaru 5
Asali: Facebook

"Tawagar sojojin ta fuskanci mayakan da karfin makaman da suke da su, kuma sun karasa sansanin soji na 156 bayan mayakan Boko Haram sun ji azaba, sun gudu saboda an fi karfinsu.

DUBA WANNAN: Gwamnati ta gano biliyan N4.3 da aka boye tsawon shekaru 10 a wani asusun sirri

"Ba mu tabbatar da adadin makiyan da dakarun soji su ka kashe ba, amma an zubar da jini a kewayen sansanin da aka yi bata kashi.

"Sojoji biyu daga cikin dakarun sansanin bataliya ta 156 sun rasa ransu, yayin da uku daga cikin tawagar da aka kaiwa harin kwanton bauna suka rasa ransu. Yanzu komai ya daidaita a Mainok, babu sauran wani tarnaki," a cewar rahoton.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel