Buhari ya amince da bude sabbin kwalejin ilimi na tarayya (FCE) a jihohi 6

Buhari ya amince da bude sabbin kwalejin ilimi na tarayya (FCE) a jihohi 6

Gwamnatin tarayya (FG) ta amince da bude sabbin kwalejin horon malamai guda shidda; daya a kowanne bangare 6 na kasa.

Hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad, ya tabbatar da hakan a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na tuwita a daren ranar Alhamis.

Kazalika, kakakin ma'aikatar ilimi, Ben Gooong, ya tabbatarwa da jaridar PremiumTimes hakan a daren ranar Alhamis.

Za a bude sabbin kwalejojin ne a jihohin Bauchi, Benuwe, Ebonyi, Osun, Sokoto da Edo.

A wata takarda mai dauke da sa hannun babban sakataren ma'aikatar ilimi, Sunny Echono, ya ce an tsayar da ranar 11 ga watan Mayu domin ziyartar wuraren da za a bude kwalejojin a jihohin.

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa ranar Alhamis, mamba a majalisar wakilai, Honarabul Farah Dagogo, ya bayyana shirin gwamnatin tarayya na cigaba da ciyar da dalibai daga gidajensu a matsayin sabon salon damfara.

DUBA WANNAN: Obasanjo ya bayyana irin mawuyacin halin da 'yan Afrika za su shiga bayan COVI-19

Ministar walwala, jin kai da jin dadin 'yan kasa, Sadiya Umar Farouq, ta bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta cigaba da tsarin nan na ciyar da dalibai duk da an rufe makarantu saboda annobar korona.

A cewar ministar, an bullo da sabon tsarin cigaba da ciyar da dalibai daga gidajensu.

Sai dai, dan majalisa Dagogo ya ce yin hakan wani salo ne kawai na cin hanci a karkashin gwamnatin da ke ikirarin yaki da rashawa.

Dagogo, mamba mai wakiltar mazabar Degema/Bonny a majalisar wakilai, ya ce kafewar gwamnati na cigaba da tsarin ciyarwar, duk da an rufe makarantu, ya nuna cewa an shirya damfarar 'yan Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel