Batun cigaba da ciyar da dalibai daga gidajensu salon damfara ne kawai - Dan Majalisa
- Ministar walwala, jin kai da jin dadin 'yan kasa, Sadiya Umar farouq, ta ce gwamnati za ta cigaba da shirin ciyar da dalibai duk da an rufe makarantu saboda annobar korona
- Sai dai, mamba a majalisar wakilai, Honarabul Farah Dagogo, ya bayyana hakan a matsayin sabon salon damfarar 'yan Najeriya
- Ya yi kira ga gwamnati ta yi amfani da kudaden wajen bunkasa bangaren kiwon lafiya da yaki da annobar cutar korona
Mamba a majalisar wakilai, Honarabul Farah Dagogo, ya bayyana shirin gwamnatin tarayya na cigaba da ciyar da dalibai daga gidajensu a matsayin sabon salon damfara.
Ministar walwala, jin kai da jin dadin 'yan kasa, Sadiya Umar Farouq, ta bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta cigaba da tsarin nan na ciyar da dalibai duk da an rufe makarantu saboda annobar korona.
A cewar ministar, an bullo da sabon tsarin cigaba da ciyar da dalibai daga gidajensu.
Sai dai, dan majalisa Dagogo ya ce yin hakan wani salo ne kawai na cin hanci a karkashin gwamnatin da ke ikirarin yaki da rashawa.
Dagogo, mamba mai wakiltar mazabar Degema/Bonny a majalisar wakilai, ya ce kafewar gwamnati na cigaba da tsarin ciyarwar, duk da an rufe makarantu, ya nuna cewa an shirya damfarar 'yan Najeriya.
A cikin jawabi da dan majalisar ya fitar ranar Laraba, ya bukaci gwamnati ta dakatar da shirin tare da yin amfani da biliyoyin da aka ware domin hakan wajen bunkasa bangaren kiwon lafiya yayin da ake fama da annobar ta korona.
Ya bayyana cewa kamata ya yi a yi amfani da kudaden ciyarwar wajen daukan nauyin binciken samar da magunguna da rigakafin cutar korona.
DUBA WANNAN: Tsare matashi a kan tsohon layin wayar diyar Buhari: Kotu ta ci tarar DSS N10m
"Bayan sauraron ra'ayin jama'ar da nake wakilta da na sauran wasu mazabu, ina mai kira ga gwamnatin tarayya a kan ta sake tunani a kan shirin cigaba da ciyar da dalibai a wannan lokaci da aka rufe makarantu.
"Sabanin cigaba da shirin a wannan lokaci, kamata ya yi gwamnati ta yi amfani da kudaden da aka ware wajen inganta bangaren kiwon lafiya, musamman wajen yaki da annobar korona," a cewar honarabul Dagogo.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng