Katsinawa sun kwaikwayi NCDC, sun fara fitar da alkaluman ta'adin 'yan bindiga a kullum

Katsinawa sun kwaikwayi NCDC, sun fara fitar da alkaluman ta'adin 'yan bindiga a kullum

Mazauna karamar hukumar Faskari a jihar Katsina sun fara fitar da alkaluman irin ta'asar da 'yan bindiga ke tafkawa kowacce rana a jihar Katsina.

A ranar Laraba ne wasu 'yan bindiga dauke da mugayen makamai suka kai wani hari a kauyukan Daudawa da Angwan Baki a karamar hukumar Faskari, inda suka sace mutane biyar tare da kashe wasu mutane biyu.

A 'yan kwanakin baya bayan nan, 'yan bindiga na cigaba da kisa, sace mutane, fyade tare da lalalta dukiyar al'umma a sassan jihar Katsina.

Sabon salon, wanda mazauna jihar suka dauka, zai ke wallafa adadin mutanen da 'yan bindiga suka kashe ko suka sace ko kuma suka raba da gidajensu, kamar yadda hukumar NCDC ke fitar da alkaluma a kan annobar korona a kullum.

Katsinawa sun kwaikwayi NCDC, sun fara fitar da alkaluman ta'adin 'yan bindiga a kullum

Katsinawa sun kwaikwayi NCDC, sun fara fitar da alkaluman ta'adin 'yan bindiga a kullum Hoto: SaharaReporters
Source: UGC

A jiya, Laraba, ne Legit.ng ta wallafa rahoton cewa mataimakin kakakin majalisar jihar Katsina, Shehu Tafoki ya samu damar yi wa zauren majalisa jawabi amma sai ya fashe da kuka a kan rashin tsaron da ya addabi mazabar Faskari.

Yankunan sun saba samun hare-haren 'yan bindiga, masu garkuwa da mutane da duk wani nau'in rashin tsaro.

DUBA WANNAN: Obasanjo ya bayyana irin mawuyacin halin da 'yan Afrika za su shiga bayan COVI-19

A makon da ya gabata, mutum biyar suka halaka sakamakon hare-haren da aka kai a kananan hukumomin Faskari da Sabuwa.

Tafoki, wanda ke wakiltar mazabar Faskari a majalisar jihar, ya ce ba a samun rana daya a halin yanzu da za ta wuce ba tare da an samu labarin kai hari a yankin ba.

Kamar yadda yace, karamar hukumar Faskari a halin yanzu za a iya kwatanta ta da Maiduguri, "Ko a daren jiya 'yan bindiga sun kai hari garin Daudawa inda suka yi garkuwa da mutum 4 sannan suka raunata wasu."

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, Tafoki na wannan jawabin ne yayin da ya fashe da kuka a zauren majalisar, lamarin da yasa ya kasa ci gaba da jawabin don haka ya koma mazauninsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel