Coronavirus: Aisha Buhari da sauran wadanda suka bayar da gudunmuwa wajen gina babbar cibiyar killace marasa lafiya a Najeriya
- Ministan birnin tarayya, Muhammad Musa Bello, ya bude babbar cibiyar killace masu cutar korona a Najeriya
- Manyan wadanda suka ba da gudunmuwa wajen gina wannan cibiya sun hadar da Kamfanin Julius Berger, uwargidan shugaban kasa; Aisha Buhari da sauransu.
- Babbar cibiyar mai cin gado 506 gini ne mai hawa hudu a yankin Idu da ke Abuja
A ranar Talata, 12 ga wata Mayu, aka kaddamar da babbar cibiyar killace masu cutar korona a babban birnin kasar na tarayya.
Ministan birnin tarayya, Muhammad Musa Bello, shi ne ya jagoranci bikin bude wannan kayatacciyar cibiya ta killace masu cutar korona wadda babu mai girmanta a duk fadin kasar.
Kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito, an kaddamar da cibiyar ne mai cin gado 506 a yankin Idu da ke Abuja domin killace mazauna birnin da cutar korona ta harba.
Baya ga tanadin ingatattun kayan jinya na zamani, an kuma kayata cibiyar ne da wasu ababe na more rayuwa domin shakatawa da kuma walwalar masu jinya da wadanda ake jinya.
Binciken jaridar Legit.ng ya gano cewa, tsohon ministan makamashi, Aliyu Modibbo Umar, wanda ya kasance shugaban kwamitin kwararru masu ba ministoci shawarwari, ya bayar da gagarumar gudunmuwa.
Dr. Modibbo da 'yan kwamitinsa sun ba da gudunmuwar kwarewa, kudi, da kayayyaki bila adadin wajen ginin wannan babbar cibiya.
KARANTA KUMA: Ana cece-kuce kan wani mangwaro kwaya daya da aka siyar N1,300
Wadanda suka ba da gudunmuwa sun hadar da:
Kamfanin Julius Berger - Gadaje 150
Aisha Buhari - Gadaje 100
Bankin Polaris - Gadaje 100 da kayayyaki
Gidauniyar FATE - Gadaje 50 da kayayyaki
Kamfanin kere-kere na kasar China; CCECC - Kayayyakin bandaki
AEDC (Abuja Electrical Distribution Company) - Kayan lantarki
IHS towers - Na'ura mai taimakon numfashi
Aliyu Modibbo Umar da Mohammed Jibril - Akwatin talabijin na zamani 258
Salini Nigeria Ltd, HITS Furniture Ltd, Yaliam Press, da Aishatu Dahiru Ahmed duk sun bayar da gudunmuwa.
Abubuwan da cibiyar ta kunsa:
Gini mai hawa hudu
Dakunan zaman jira kira na ma'aikatan lafiya
Wuraren gado 506
Kwararrun ma'aikatan lafiya
Na'urori masu taya numfashi
Motocin ambulans na daukar marasa lafiya
Dakuna masu raba da kwandishan
Jami'an tsaro
Wuraren wanka da bayan gida
Firizai
Hasken lantarki
Talibijin da aka hada wa tashoshin kallace-kallace
Dakunan tsaftace kayayyaki
Wurin cin abinci
Kyamarorin CCTV da sauransu.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng