NANS, NUT, CPE, da Iyaye sun damu da kudin da ake kashewa ‘Yan Makaranta
Jama’a sun nuna damuwarsu a game da makudan miliyoyin da gwamnatin tarayya ta ke ikirarin kashewa wajen ciyar da ‘daliban makarantun gwamnati a daidai lokacin da ake hutu.
Jaridar Vanguard ta ce Mutane su na ganin yunkurin ci da ‘dalibai a wannan marra da aka rufe duk wasu makarantu saboda annobar cutar Coronavirus, ba zai iya haifar da ‘da mai ido ba.
A halin yanzu gwamnatin Najeriya ta na fama da karancin kudi, amma ta dage a kan cewa za ta cigaba da bada abinci kullum ga ‘yan makaranta a cikin wasu jihohi 31 da ke fadin kasar.
Kungiyoyi irinsu NANS na ‘daliban Najeriya, da NUT ta malaman makaranta da kuma wasu kungiyoyin iyayen yara irinsu CPE su na ganin cewa wannan shiri ba zai kai ko ina ba.
Shugaban kungiyar NANS na shiyyar kudu maso yamma, Kwamred Kappo Samuel Olawale, ya ce babu yadda za a iya dabbaka wannan tsari a Najeriya a lokacin da yara su ke gidajensu.
KU KARANTA: Za mu lura da yadda za a kashe kudin da mu ka ba Najeriya – Amurka
“Wannan shiri ba zai yi aiki ba, a wurina yaudara ce kurum wanda za ta ci makudan kudi. Gidaje nawa masu abinci za su je tun da ‘yan makaranta ba za su taru ba.” Inji Kappo Olawale.
Kappo Olawale ya ce idan aka fadawa masu rabon abincin su je gidajen ‘daliban, wannan zai sa a kara kashe kudin zirga-zirga, idan aka ce ‘dalibai su fita, za a samu cinkoson da ba a so.
A ra’ayin shugaban kungiyar Malamai na Legas, Otunba Adesina Adedoyin ko da hakan zai yiwu, da kamar wuya. Shugaban na NUT ya ce tun farko akwai matsala tattare da wannan tsari.
Misis Yinka Ogunde, wanda shugabar wata kungiya ce ta iyaye mai suna CPE, ta nuna shakkar ta game da yunkurin da gwamnatin ta ke yi. Ogunde ta ce ba a san inda yaran su ke zama ba.
Evans Ufeli ya fadawa jaridar: “Gwamnatin nan ta daina ba Najeriya kunya.” Wasu su na ganin abin da ya fi shi ne gwamnati ta taimakawa iyayen yaran da su ke cikin mawuyacin hali.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng