Gambari ba zai iya shawo kan matsalar 'Cabals' ba a Najeriya - Farfesa Adibe

Gambari ba zai iya shawo kan matsalar 'Cabals' ba a Najeriya - Farfesa Adibe

Jideofor Adibe, farfesan kimiyyar siyasa, ya ce Ibrahim Gambari, sabon shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa ba zai iya shawo kan matsalar masu juya gwamnati ba.

Gambari, tsohon ministan harkokin waje ya zama shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa a ranar Laraba.

A yayin zantawa da shirin siyasa a yau da gidan talabijin din Channels, Adibe ya ce duk kwarewar kungiya dole ne a samu wasu da ke da ta cewa tare da juya ta.

Farfesan ya ce dole ne samu wata karamar kungiya da za ta dinga fadi a ji. Ya ce nan ba da jimawa ba Gambari zai shiga cikin 'Cabals'.

Gambari ba zai iya shawo kan matsalar 'Cabals' ba a Najeriya - Farfesa Adibe
Gambari ba zai iya shawo kan matsalar 'Cabals' ba a Najeriya - Farfesa Adibe Hoto: Bashir Ahmad
Asali: Twitter

"Farfesa Gambari ba zai iya shawo kan matsalar 'miyagu' ba a gwamnatin nan. Kowacce kungiya, komai iya mulkar mutane da ta yi da zabinsu, dole a samu wasu masu juya ta," yace.

"Don haka dole a samu wata karamar kungiya wacce a kowanne lokaci tana iya magana da gwamnati. Tana iya zartarwa tare da hanawa. Wadannan su ake kira da 'Cabals'.

"Kowa zai iya shigewa cikin miyagun, komai jimawa kuma kokai dadewa."

KU KARANTA KUMA: Sabon sautin murya: Muhimman sakonni 5 da Shekau ya fitar

Farfesan ya ce dama can 'yan Najeriya ba su tsammanin wani abu mai girma daga wurin sa.

"Shugaban kasar yana da kungiyar masu bada shawara a kan tattalin arziki, yana da ministan kudi, yana da kwamitin yaki da cutar coronavirus da sauransu. Aikinsa kuwa yanzu shine bada shawara," yace.

A baya mun ji cewa Sabon shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari ya ce abinda zai bai wa fifiko na farko shine biyayya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ba jama'a ba.

Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasar ya sanar da hakan ne yayin da yayi tattaunawa takaitacciya da manema labaran gidan gwamnati a fadar shugaban kasar da ke Abuja.

Ya fara da mika sakon godiyarsa da Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya ga cancantarsa na mate wannan gurbin. Ya ce zai yi iyakar bakin kokarinsa wajen hidimtawa shugaban kasar, jaridar The Nation ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng