Albashi: SSANU da NAAT sun shirya gwabzawa da Gwamnati a kan tsarin IPPIS

Albashi: SSANU da NAAT sun shirya gwabzawa da Gwamnati a kan tsarin IPPIS

Kungiyoyin ma’aikatan jami’an Najeriya wadanda ba su aikin koyarwa sun shirya fafatawa da gwamnatin tarayya a game da matsalar da su ke fuskanta wajen samun albashinsu.

Jaridar Vanguard ta ce ma’aikatan su na kukan cewa abubuwa ba su tafiya daidai tun bayan da su ka shiga cikin tsarin biyan albashi na IPPIS da gwamnati ta kawo kwanakin baya.

Shugabannin kungiyoyin SSANU da na NAAT watau manyan ma’aikatan jami’a da na malaman dakunan binciken fasaha sun ce shiga tsarin IPPIS ya zo masu da ciwon kai iri-iri.

Duk da cikas da ake fuskanta wajen samun albashi, shugaban kungiyar SSANU, Kwamred Samson Ugwoke, ya yi kira ga ‘ya 'yansa su sa hakuri game kuskuren da ake samu.

Ma’aikata su na korafin cewa wani lokaci ana zaftare masu kudi masu tsoka daga albashin na su, ko a biya su wani albashin na dabam, ko kuma a gaza ba su takardun biyan kudinsu.

A na sa bangare, shugaban NAAT, Kwamred Ibeji Nwokoma ya koka da cewa har yanzu ba a biya su albashin watan Afrilu ba, wannan ya zo a daidai lokacin da ake faman zaman-gida.

KU KARANTA: Farfesa Zulum ya bude Jihar Borno, ya cire takunkumin zaman-gida

Albashi: SSANU da NAAT sun shirya gwabzawa da Gwamnati a kan tsarin IPPIS
Ministan ilmi Adamu Adamu Hoto daga: Premium Times
Asali: UGC

Ibeji Nwokoma ya ke cewa bayan sun kai kukan cewa an zaftare masu wasu alawus dinsu a albashin watan Fabrairu sai kuma yanzu ga shi an gagara biyan albashin watan Afrilu.

Kwamred Nwokoma ya bayyana cewa bayan shigar su tsarin IPPIS sun fara ganin ana cire masu makudan kudi da sunan haraji da kuma kudin fansho, da harajin kungiya da kudin gida.

“Mun yi maza mun sanar da ofishin IPPIS game da wannan, kuma mu ka gana da darektan. Ana cikin kokarin gyara wannan lamari ne sai annobar COVID-19 ta barke.” Inji Nwokoma.

Nwokoma ya ce: “Abin takaici, har a watan Maris ba a gyara wadannan kura-kurai da ake samu ba. Ina tabbatar maku cewa za a maida wadannan alawus, a biya mu kudin da mu ke bi.”

SSANU ta ce annobar COVID-19 ta sa ba a iya warware matsalolin da ake fuskanta ba, amma da zarar abubuwa sun dawo daidai, za su zauna domin ganin gwamnati ta yi abin da ya dace.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel