'Yan bindigar da suka sace kaftin Gana sun nemi a biyasu N20m kudin fansa - 'Yan sanda

'Yan bindigar da suka sace kaftin Gana sun nemi a biyasu N20m kudin fansa - 'Yan sanda

Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Ondo ta bayyana cewa 'yan bindigar da suka yi garkuwa da kaftin a rundunar soji sun nemi a biyasu miliyan N20 a matsayin kudin fansa.

A cewar kakakin rundunar 'yan sandan jihar Ondo, ASP Tee-Leo Ikoro, an sace kaftin D. Gana da sauran wasu mutane uku a kan hanyar Auga zuwa Akunnu a yankin karamar hukumar Akoko ta gabas.

Ikoro ya ce an sacesu ne da misalin karfe 4:00 na safiyar ranar Talata yayin da suke kan hayarsu ta dawowa daga Abuja.

"Ma su garkuwa da mutanen, wadanda ke ofireshon a kan iyakar jihohin Ondo da Edo, sun tuntubi iyalan mutanen da suka sace ranar Laraba tare da neman a biyasu N20m a matsayin kudin fansar sakin mutanen hudu da suke rike da su," a cewar Ikoro.

Mista Ikoro ya bayar da tabbacin cewa dakarun rundunar soji da hadin gwuiwar jami'an 'yan sanda a jihar Ondo sun kewaye jejin yankin da aka sace mutanen domin kubutar da su da kuma kama 'yan ta'addar.

"Kwamishinan 'yan sanda na jihar Ondo, Undie Adie, ya bawa jami'an 'yan sanda umarnin kewaye jejin domin nemo 'yan ta'ddar da kuma kubutar da mutanen da suka sace.

"Tuni mun fara bincike a kan lamarin, amma duk da haka mu na neman muhimman bayanai da zasu iya taimakawa wajen kama 'yan ta'addar," a cewarsa.

'Yan bindigar da suka sace kaftin Gana sun nemi a biyasu N20m kudin fansa - 'Yan sanda
Kwamishinan 'yan sandan jihar Ondo
Asali: Twitter

A wani labarin da ya shafi rundunar soji da Legit.ng ta wallafa, rundunar sojin, a karkashin atisayen OPSH a jihar Filato, ta tabbatar da mutuwa wani matashi, Rinji Bala, mai shekaru 20, wanda ya ke aji uku a jami'ar Jos.

DUBA WANNAN: An bude Masallatan kasar Iran albarkacin kwanaki 10 na karshen Ramadan

A ranar Talata ne dakarun rundunar OPSH suka harbi Bala, wanda aka fi sani da 'Bobo', a ofishinsu da ke kan titin zuwa Zaria a garin Jos, babban birnin jihar Filato.

Da ya ke tabatarwa da kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) faruwar lamarin, kakakin rundunar OPSH, Ibrahim Shittu, ya ce basu ji dadin abinda ya faru ba.

A cewar Shittu, mai mukamin manjo a rundunar soji, jami'an rundunar OPSH sun samu kiran kar ta kwana a kan al'amuran wasu batagari, har ma suka kama matasa bakwai da ake zagi suna daga cikinsu.

Ya bayyana cewa daga baya sun sallami Bala da wasu sauran matasa hudu bayan sun gano cewa basu da laifi, amma a hanyarsu ta fita daga ofishin, sai wani soja ya yi kuskuren tunanin cewa guduwa zasu, lamarin da yasa ya bude musu wuta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng