Yawo da ake faman yi da Almajirai ya sabawa hakkin su na ‘yan kasa – ‘Yar Majalisa

Yawo da ake faman yi da Almajirai ya sabawa hakkin su na ‘yan kasa – ‘Yar Majalisa

- Majalisar Wakilai ta nemi gwamnatin tarayya ta sa a daina yawo da Almajirai

- ‘Yan majalisar kasar sun ce maida yaran zuwa jihohinsu da ake yi ya saba doka

- Aishatu Jibril Dukku ta ce wannan na iya kara zuga wutar annobar COVID-19

Wasu ‘yan majalisar wakilan tarayya sun yi kira ga gwamnatin tarayya da cewa ta hana yawo da ake yi da almajirai tsakanin jihohin kasar yayin da ake fama da annobar COVID-19.

‘Yan majalisar kasar sun bijiro wannan magana ne yayin zaman farko da su ka yi a makon nan. Majalisar ta zauna a jiya ranar 12 ga watan Mayu, 2020 a birnin tarayya na Abuja.

Aishatu Jibril Dukku ta soki yadda ake yawo da wasu almajirai daga wannan jiha zuwa wannan jiha. ‘Yar majalisar ta jam’iyyar APC ta ce yin hakan keta alfaramar ‘Dan Adam ne.

Kamar yadda mu ka samu labari, wani ‘dan majalisan PDP na yankin Akwa-Ibom ya goyi bayan wannan korafi na Aishatu Jibril Dukku, ya ce lallai yin hakan ba daidai ba ne.

KU KARANTA: Za a binciki abin da ya hana COVID-19 shiga wasu Jihohin 2 a Najeriya

Honarabul Aishatu Jibril Dukku mai wakiltar Dukku da Nafada a jihar Gombe ta fadawa abokan aikin ta cewa dokar Najeriya ta ba kowane 'dan kasa damar zama duk inda ya ga dama.

Tun kwanaki aka samu wasu gwamnoni a yankin Arewa su na dauke almajirin da ke cikin jihohinsu, su na maidasu ainihin garuruwansa da sunan yaki da annobar Coronavirus.

Tsohuwar ministar ilmin ta nuna cewa yunkurin da ake yi na maida almajiran inda su ka fito zai zama an yi aikin banza domin akwai yiwuwar hakan ya taimakawa yaduwar cutar.

Hon. Dukku ta ke cewa yadda ake cunkusa almajiran a motaci wajen maida su gidajen iyayensu zai sa yaduwar mummunar cutar ta COVID-19 da ake gudu ya karu a fadin kasar.

Dukku wanda ta ke majalisar tarayya tun 2015 ta bayyana cewa akwai cin zarafi wajen hanyar da jihohi ke bi wajen tattara wadannan kananan yara da su ke karatun almajiranci.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Nigeria

Online view pixel