Sarkin Ilorin ya yi godiya ga Buhari kan nada dan jihar a matsayin sabon shugaban ma’aikatansa

Sarkin Ilorin ya yi godiya ga Buhari kan nada dan jihar a matsayin sabon shugaban ma’aikatansa

Sarkin Ilorin, Ibrahim Sulu-Gambari ya mika godiyarsa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan nada Ibrahim Gambari a matsayin sabon shugaban ma'aikatan fadarsa.

Gambari, wanda farfesan kimiyyar siyasa ne kuma tsohon wakilin Najeriya a majalisar dinkin duniya dan asalin jihar Kwara ne.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa Gambari zai tabbata a matsayin sabon shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa a ranar Laraba.

A wata takarda da ta fita a ranar Laraba, Sulu-Gambari ya kwatanta nadin da babban karramawa ga jama'ar Ilorin da Kwara gaba daya.

Sarkin Ilorin ya yi godiya ga Buhari kan nada dan jihar a matsayin sabon shugaban ma’aikatansa

Sarkin Ilorin ya yi godiya ga Buhari kan nada dan jihar a matsayin sabon shugaban ma’aikatansa Hoto: Thisday
Source: Twitter

Ya ce zaben Gambari a wannan matsayin zai bayyanar da kwarewarsa tare da gogewarsa a fannin mulkin wanda zai kasance babbar gudumawa ga gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Hakan zai tabbatar da shugabanci na gari wanda zai kawo romon damokaradiyya ga jama'a kai tsaye.

"Ta gogewarsa da kwarewarsa a matsayin malami, tsohon ministan, tsohon shugaban majalisar zartarwa ta jami'a, yariman masarautar Alimi, mutum mai iyali kuma shugaban jama'a na da matukar amfani," yace a takardar.

A yayin taya Gambari murna a kan wannan nadin, sarkin ya yi masa fatan sauke nauyin da ya hau kansa.

KU KARANTA KUMA: Za a cigaba da sallar Juma'a a Masallatan jihar Jigawa

Basaraken ya tabbatar da cewa sabon shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasar ba zai bada kunya ba don zai iya sauke nauyin da ke kansa.

A baya mun ji cewa tsohon sakataren majalisar dinkin duniya, Farfesa Ibrahim Gambari ya zama magajin marigayi Abba Kyari. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada tsohon sakataren majalisar dinkin duniyan a matsayin shugaban ma'aikatan fadar sa.

Gambari dan asalin jihar Kwara ne kuma ya yi tsohon ministan harkokin waje tsakanin 1984 zuwa 1985.

Farfesan na da babbar shaidar kwarewa da jajircewa. Yana da shekaru 78 a duniya a yanzu da ya maye gurbin marigayi Abba Kyari.

Farfesa Gambari ya yi aiki tukuru a yayin da yake sakataren majalisar dinkin duniya, kuma mai bada shawara na musamman ga babban sakataren nahiyar Afrika tsakanin 1999 zuwa 2005.

Mutum ne sananne a gida da wajen kasar nan. Shine shugaban majalisar zartarwa ta jami'ar jihar Kwara a halin yanzu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel