Mai martaba Muhammadu Sanusi II ya yi ta’aziyyar ‘Dan Iya Yusuf Bayero

Mai martaba Muhammadu Sanusi II ya yi ta’aziyyar ‘Dan Iya Yusuf Bayero

A cikin karshen makon da ya gabata ne Ubangiji ya karbi ran Alhaji Yusuf Bayero wanda ya kasance ya na rike da sarautar ‘Dan Iyan Kano na kusan tsawon shekaru 30.

A ranar Lahadi, 10 ga watan Mayu, 2020, wajen karatun da ya ke yi, tsohon sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya aikawa 'yanuwa da mutanen Kano da ta’aziyyar Kakansa.

A ta’aziyyar, Malam Muhammadu Sanusi II ya bayyana Alhaji Yusuf Bayero a matsayin bawan Allah, masani mai hidima ga addini kuma mai yi wa al’ummar kasar Kano bauta.

Muhammadu Sanusi II ya bayyana cewa marigayin shi ne babban ‘dan da ya rage a cikin ‘ya ‘yan sarki Alhaji Abdullahi Bayero. Ya ce ya dade sosai ya na fama da larurar ciwon kafa.

Malam Sanusi II ya ce marigayin ya yi gadon mahaifinsa wajen kula da addini. Wannan ya sa mai martaban ya ke cewa an yi rashi sosai a gidan Bayero da kuma daukacin kasar Kano.

KU KARANTA: Tsohon Sarki Sanusi II ya samu 'Diya mace a wajen Amaryarsa

Sai dai tsohon sarkin na Kano ya koka da abin da ya kira zaluncin da aka yi wa marigayin. Sanusi II ya nuna an wulakanta Yusuf Bayero bayan gwamnati ta kirkiri wasu masarautu.

Yusuf Bayero ya na cikin gidan tsohon sarkin Kano Muhammadu Abbas, aka fatattake sa a dalilin kin yi wa sabon sarki (na Gaya) da aka nada mubaya’a, a cewar Malam Sanusi II.

Kamar yadda wani bidiyo da shafin Masarautar Kano ta wallafa a Facebook ya nuna, Sanusi II ya ce: “Allah zai saka masa (Alhaji Yusuf Bayero) a game da zaluncin da aka yi masa.”

Bayan haka mai martaba ya ja kunne inda ya ce kamar yadda ‘Dan Iya ya cika, kowa zai mutu har da wadanda su ka yi masa wulakanci, kuma Ubangiji zai yima kowane hisabin aikinsa.

Sarkin da aka tunbuke a watan Maris din bana ya ce iyakarsa zura idanu a kan abubuwan da ke faruwa, a karshe ya yi addu’ar Allah ya sa marigayi Alhaji Yusuf Bayero ya tafi a sa’a.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel