COVID-19: El-Rufai ya sanar da mutuwar wani babban mutum a jihar Kaduna

COVID-19: El-Rufai ya sanar da mutuwar wani babban mutum a jihar Kaduna

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya sanar da rasuwar majinyata biyu sakamakon annobar Coronavirus, kwanaki takwas bayan sanar da mutuwar farko da jihar ta fuskanta sakamakon cutar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa a halin yanzu jihar Kaduna ta rasa mutum uku sakamakon annobar Coronavirus.

Na farkon ma'aikacin gwamnati ne wanda ya yi ritaya kuma yana da wasu ciwuka kafin annobar. Ya boye tarihin tafiyar da yayi zuwa Kano ko da ya ziyarci wani asibiti mai zaman kansa kafin ya koma na gwamnati.

Gwamna El-Rufai ya sanar da mace-macen ne a shafinsa na twitter. Ya ce daya daga cikin mamatan babban ma'aikacin jihar ne daga karamar hukumar Makarfi. Dayar kuwa mace ce daga karamar hukumar Zaria ta jihar.

COVID-19: El-Rufai ya sanar da mutuwar wani babban mutum a jihar Kaduna
COVID-19: El-Rufai ya sanar da mutuwar wani babban mutum a jihar Kaduna Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Duk da bai bayyana sunayen mamatan ba, a daren Alhamis gwamnan ya tabbatar da karuwar mutum bakwai masu cutar kamar yadda NCDC ta sanar.

Daga cikinsu kuwa akwai wani babban mutum a jihar wanda ya karba baki masu tarin yawa.

Kamar yadda ya sanar a shafinsa na twitter, El-Rufai ya ce a halin yanzu jihar Kaduna na da mutum 87 da aka tabbatar da suna dauke da cutar.

KU KARANTA KUMA: COVID-19: An aiko wa Najeriya da maganin Madagascar

Ya ce mutum biyun da NCDC ta sanar da kamuwarsu a jihar da daren Asabar, akwai namiji daga Igabi sai kuma mace daga karamar hukumar Chikun.

Kamar yadda NCDC ta sanar, mutum 98 ne suka kamu da muguwar cutar a jihar Kaduna.

A wani labari na daban, gwamnatin jihar Bauchi ta yi bayani a kan rahoton mace-macen da ke faruwa a yankin Azare na jihar.

A cewarta, yanayin zafin gari ne ke kawo mace-macen ba annobar Coronavirus ba.

Mataimakin Gwamnan jihar, Baba Tela ya sanar da manema labarai a ranar Lahadi cewa tuni aka yi bincike kuma an gano zuzuta yawan mace-macen ake yi.

Kamar yadda gidan talabijin din Channels ya bayyana, mataimakin Gwamnan wanda shine shugaban kwamitin yaki da cutar coronavirus na jihar, ya ce kafafen sada zumuntar zamani na ruwaito cewa mutum 300 ne suka rasu a mako daya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel