Gwamnan Jihar Ebonyi ya dakatar da Kwamishina da Sakatare na wata daya

Gwamnan Jihar Ebonyi ya dakatar da Kwamishina da Sakatare na wata daya

Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya bada umarnin dakatar da kwamishinansa na harkokin kananan hukumomi da masarautu Samuel Okoronkwo, saboda wasa da aiki da ya yi.

Hukumar dillacin labarai na kasa ta NAN ta ce ana zargin kwamishinan da sakaci ne wajen sha’anin tsaron rufe iyakokin jihar yayin da ake fama da annobar cutar nan ta COVID-19.

A wata sanarwa da ya yi jiya, mai girma gwamnan ya bukaci kwamishinan ya zauna a gida na tsawon wata guda. Wannan ya na nufin Okoronkwo ba zai samu albashin wata guda ba.

Gwamnan ya bada wannan sanarwa ne da kansa ta wani jawabi da ya fitar a kafafen sadarwa na zamani. Umahi ya rattaba hannu a jawabin dakatar da wannan kwamishina daga aiki.

Gwamna David Umahi ya kuma dakatar da sakataren din-din-din na ma’aikatar kananan hukumonin jihar, Dr. Augustine Nwuzor a dalilin tarayya da kwamishinan wajen yin laifi.

Kwamishinan yada labarai na Ebonyi, Uchenna Orji ya tabbatar da wannan dakatarwa da gwamnan ya yi wa abokin aikinsa. Har ta kai gwamnan ya yi barazanar tsige jami'an.

KU KARANTA: Ba za mu rufe Ebonyi saboda annobar COVID-19 ba - Inji Umahi

Umahi ya ce idan har ba a samu wani cigaba ba bayan wata guda, zai sauke kwamishinan daga kujerarsa. Haka zalika gwamnan ya ce Dr. Augustine Nwuzor zai bar ofis idan ya yi wasa.

“An dakatar da duk wasu shugabannin kananan hukumomin Afikpo da Ivo, su mika takardunsu ga wadanda su ka fi dadewa a ofishinsu, su kuma mika motocin aikinsu.” inji gwamnan.

Ya ce: “Duk masu rike da kujera a kananan hukumomin za su rika karbar rabin albashi har sai abubuwa sun mike. Wannan ya shafi sarakunan gargajiya da ma’aikatan gwamnati.”

Umahi ya kuma bayyana cewa ya tare wasu motoci goma da ke dauke da jama’a daga jihohin Abia, Ribas da Legas. Abin da ya gani a iyakokin jihar ya sa hankalin gwamnan ya tashi.

Har ila yau, gwamnan Ebonyi ya dakatar da duk wasu kungiyoyin unguwanni, sannan ya yi alkawarin ruguza su muddin abubuwa ba su sake zane a cikin wannan watan Mayun ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel