An soma saida mana litar fetur a kan N108 – Shugaban kungiyar IPMAN

An soma saida mana litar fetur a kan N108 – Shugaban kungiyar IPMAN

- Kungiyar IPMAN ta ce an fara saida mata litar man fetur a kan N108

- Kwanan nan gwamnatin Najeriya ta rage N5 daga cikin farashin sari

- Babu tabbacin cewa wannan zai sa gidajen mai su rage kudin mansu

Shugaban kungiyar nan ta IPMAN ta dillalan man fetur masu zaman kansu a Najeriya, Chinedu Okoronkwo, ya ce ‘yan kungiyarsa sun fara sayen litar mai a kan sabon farashi.

A ranar Lahadin nan ne Chinedu Okoronkwo ya bayyanawa ‘yan jarida cewa sun fara sayen kowane litar man fetur a kan N108 a manyan tashoshin man da ake da su a kasar.

Mista Chinedu Okoronkwo ya yaba da matakin da gwamnati ta dauka na rage farashin litar man fetur daga N113 zuwa N108. Wannan ragi da aka yi ya shafi ‘yan sari ne a Najeriya.

“Mun fara samun mai a N108 kamar yadda NNPC ya sanar. Abin a yaba ne, amma ba za a ayi farin ciki da wannan tsari ba, domin za ka saye kaya ne da araha, ka saida da tsada.”

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari ta ragewa dillalai kudin man fetur a Najeriya

“Sabon farashin zai taimakawa manyan ‘yan sari ne kawai.” Okoronkwo ya ke fadin haka a lokacin da ya yi hira da hukumar dillacin labarai na kasa ta NAN a karshen makon jiya.

Shugaban kungiyar IPMAN ya ke cewa nan gaba za su rika shigo da man da kansu: “Idan kasuwanni su ka bude, ‘yan kasuwa za su je waje su sayo mai, su dawo gida su saida.”

Chinedu Okoronkwo ya ce farashin fetur zai lula sama idan danyen mai ya kara kudi a kasuwa. Shugaban IPMAN ya bukaci gwamnatin tarayya ta yi ta gyara matatun man kasar.

Shi kuma a na sa bangaren, shugaban kungiyar PETROAN ta ‘yan sarin mai a Najeriya, Dr. Billy Gillis-Harry, ya ce har yanzu su na sayen litar man fetur ne a kan N113 ba N108 ba.

Dr. Gillis-Harry ya ce duk da gwamnatin tarayya ta rage kudin mai a kasar tun a makon da ya gabata, har yanzu ana saida masu litar fetur ne a kan farashin da kowa ya sani a da.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel