Manyan yan wasan Najeriya 4 da suka bar addinin Kirista zuwa na Islama

Manyan yan wasan Najeriya 4 da suka bar addinin Kirista zuwa na Islama

Masana'antar shirya fina-finai ta Nollywood da ke kudancin kasar ta tara manyan jarumai kyawawa daban-daban. Wadannan jarumai sun fito daga addinai daban-daban.

Daga ciki mun zakulo maku wasu jarumai kiristoci da suka zama Musulmai.

1. Vivian Metchie

Manyan yan wasan Najeriya 4 da suka bar addinin Kirista zuwa na Islama
Manyan yan wasan Najeriya 4 da suka bar addinin Kirista zuwa na Islama Hoto: Vivian Fareedah Metchie
Source: Instagram

'Yar wasan kwaikwayo a masana'antar Nollywood Vivian Metchie ta bai wa jama'a da dama mamaki a lokacin da ta sanar da komawarta addinin Musulunci.

An haifa Vivian cikin addinin Kirista don mahaifinta da mahaifiyarta duk Kiristoci ne.

Kamar yadda ta bayyana, ta bar addinin Kirista saboda dimuwar da ta shiga kuma ta koma suna Fareedah bayan karbar kalmar Shahada.

A kalamanta: "Ra'ayina ne kuma ina gane Qur'ani fiye da Bibul. A lokaci daya Kiristanci ya fara saka ni cikin rudani da dimuwa.

"Mahaifiyar ta tana bin akidar Deeper Life amma mahaifina yana bin akidar Katolika. Na auri mabiyin cocin Redeemed amma kuma sai na lura cewa bangarorin ba daya bane. Ba zan iya lamunta ba.

"Wata kawata makusanciya ta ce matukar ina fahimtar kalaman, ba zan dinga rudewa ba. A karatuna da bincikena, kwanciyar hankali nake nema. Na kuma same shi a Qur'ani."

2. Laide Bakare

Manyan yan wasan Najeriya 4 da suka bar addinin Kirista zuwa na Islama
Manyan yan wasan Najeriya 4 da suka bar addinin Kirista zuwa na Islama Hoto: Laide Bakare
Source: Instagram

'Yar wasan Nollywood din ta koma addinin Musulunci bayan ta rabu da mijinta mabiyin addinin Kirista.

Tun bayan da Laide ta hadu da Alhaji Tunde Orilowo wanda aka fi sani da ATM, sai ta koma addinin Musulunci.

KU KARANTA KUMA: Rikicin yanki: Mutum 50 sun bace, 300 sun samu raunika, da yawa sun rasa rayukansu

3. Liz Da Silva

Jaruma Liz Da Silva Kirista ce har sai da ta haifa da da tsohon shugaban NURTW na Oshodi, Musiliu Akinsanya wanda aka fi sani da MC Oluomo.

Bayan sun rabu, ta auri wani Musulmi mai suna Olaoye. Liz bata tsawaita a addinin Kirista ba ta koma Musulma inda aka sa mata suna Aisha.

"Idan baku sani ba, ina da dangantaka mai kyau tsakanina da mahaifin da na. Tun kafin in haihu na koma Musulma kuma ake kirana Aisha saboda abinda zan haifa," Liz Da Silva ta bayyana a wata tattaunawar da aka yi da ita.

4. Adunni Ade

Fitacciyar jarumar wasannin Najeriya, Adunni Ade ta ba mabiyanta mamaki a shafin soshiyal midiya, bayan ta fito ta yi magana a kan wani bangare na rayuwarta.

Jarumar ta bayyana cewa tun da dadewa ta daina yin sharhi a kan abun da ya shafi addini, saboda abune mai matukar kaifi a gare ta. Ta kara da cewa makusantan ta na dab-da-dab ne kadai suka san wani addini ta ke yi.

Hakan ya biyo bayan fitowa da jarumar ta yi domin ta yi karin haske a kan kokwanton masu rade-radi, sannan ta bayyana cewa ita Musulma ce ta hakika.

Adunni ta bayyana cewa an haife ta a gidan Musulunci sannan an tayar da ita a kan tafarkin addinin Islama.

"Don haka ga wadanda ke ta tambaya, Eh ni Musulma ce. An haife ni a gidan Musulunci sannan an rene ni a kan tafarkin Islama. Idan kuna son sani, B2 na samu a jarrabawar WAEC.

"Mahaifina Musulmi ne wanda ke ba yaransa damar zabar duk addinin da suke so imma na Kirista ko Islama.

"Mahaifiyata Kirista ce, koda dai bata aiki da shi. Kishiyar mahaifiyata ma Kirista ce, yan uwana mata Kiristoci ne, yan uwana maza Musulmai ne,” jarumar ta rubuta.

Da ta ke ci gaba da bayani, Adunni ta bayyana cewa a wani mataki da ta kai a rayuwarta sai ta koma addininin Krista inda ta ke bauta a MFM, RCCG, CLAM, CAC, da sauran cocina.

Ta bayyana cewa yayinda ta ke duk wannan, addinin Islama bai bar jikinta ba.

Adduni ta ce tsawon wasu shekaru tana damuwa a kan abun da mutane za su ce idan ta koma Musulunci. Sai dai kuma, a watan Disamba 2016, sai ta koma addinin Islama.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel