Ba a sarki biyu a zamani daya: Wike ya yi wa shugaban 'yan sanda martani mai zafi

Ba a sarki biyu a zamani daya: Wike ya yi wa shugaban 'yan sanda martani mai zafi

A jiya ne Gwamna Nyesom Wike ya ja kunnen mataimakin kwamishinan 'yan sandan jihar, Adamu Abubakar da kakkausar murya.

Ya zargi dan sandan da zagon kasa ga dokokin hana zirga-zirga da ya kafa a kananan hukumomin Fatakwal da Obio-Akpor don hana yaduwar annobar a jihar Ribas.

Kamar yadda yace, shugaban 'yan sandan na bada wasiku ba tare da izininsa ba ga kamfanoni don su karya dokar ta-baci.

Ya tabbatar da cewa ba za a taba samun gwamnoni biyu a lokaci daya a jihar ba. Don haka ya bada umarnin damko wasu mutum 200 da aka kama da laifin karya doka a jihar.

Kamar yadda jaridar The Guardian ta bayyana, wadanda aka kama za su fuskanci hukunci mai tsauri kuma ababen hawan da aka kama za a yi gwanjonsu.

Gwamnan wanda ke duba yadda ake bin dokar a kowanne mataki na jihar, ya ce: "Abun takaici ne yadda mataimakin kwamishinan 'yan sanda na jihar na bai wa kamfanoni takardun fara aiki don take dokar jihar,"

Ya ce ba za a taba samun sarakuna biyu na a gari daya.

Ya jaddada cewa duk wata takardar amincewa da bata fito daga ofishinsa ba bata da tushe a shari'ance.

Ba za a taba samun sarakuna biyu na a gari daya ba – Gwamnan Ribas ya gargadi mataimakin kwamishinan yan sanda, Adamu Abubakar

Ba za a taba samun sarakuna biyu na a gari daya ba – Gwamnan Ribas ya gargadi mataimakin kwamishinan yan sanda, Adamu Abubakar Hoto: Govt House, Port Harcourt
Source: Facebook

A wani bangare, jam'iyyar APC ta yi kira ga gwamnan da ya farfado da ayyukan mai aikatar lafiya da wanda ya gada, Chibuike Amaechi ya bari. Hakan zai tabbatar da kokarinsa wajen kawo mafita ga jama'ar jihar.

Jam'iyyar ta jinjinawa kamfanin habaka kayayyakin man fetur na Shell da ya tallafawa jihar.

A wata takarda da shugaban jam'iyyar, Chief Eze Chukwuemeka Eze ya fitar, ya ce an saka siyasa a al'amuran asibitin koyarwa na jami'ar Fatakwal.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya ce za a yi gwanjon motocin da aka kama masu shi suna tuka su a lokacin dokar hana fita a jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 7 ga watan Mayu, a wata hira bayan ya fita rangadi don ganin yadda ake bin dokar da gwamnati ta saka.

“Kotun tafi-da-gidanka za ta hukunta wadanda suka karya dokar kuma na fada ma Atoni Janar, ya zama dole a yi gwanjon dukkanin ababen hawan da aka kama. Zuwa gobe, mai girma Atoni Janar zai tallata ababen hawan kuma za mu yi gwanjon su,” in ji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel