Hotunan masu garkuwa da mutane 23 da makamansu da rundunar 'yan sanda ta kama a Adamawa

Hotunan masu garkuwa da mutane 23 da makamansu da rundunar 'yan sanda ta kama a Adamawa

- Rundunar 'yan sanda ta kama masu garkuwa da mutane 23 tare da manyan makamansu a jihar Adamawa

- Sabon kwamshinan 'yan sanda a Adamawa, Olugbenga Adeyanju, ya ce zai yi yaki da ta'addanci da 'yan ta'adda a jihar

- Kwamishinan ya bukaci jama'a su bawa rundunar 'yan sanda hadin kai tare da basu muhimman bayanai a kan 'yan ta'adda da sauran masu laifi

A ranar Alhamis ne rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Adamawa ta yi bajakolin masu garkuwa da mutane 23 tare da manyan bindigunsu samfurin AK47 guda uku da ta kama.

Kazalika, rundunar 'yan sanda ta samu wasu manyan makamai da suka hada da bindigi mai inji (machine gun), wasu manyan bindigu masu baki biyu guda biyu, alburusai 468 da kwanson alburusai 45 duk a wurin 'yan ta'addar.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Adamawa, Olugbenga Adeyanju, ne ya sanar da hakan yayin holin masu laifin ga manema labarai a Yola, babban birnin jihar Adamawa.

A cikin watan Afrilu ne 'yan bindigar suka karbi kudin fansa da yawansu ya kai N4.5m bayan sun sace wasu mutane biyu; Ardo Kulda da Tela Bala, a kauyukan Guyaku da Golantabal a karkashin karamar hukumar Gombi.

Hotunan masu garkuwa da mutane 23 da makamansu da rundunar 'yan sanda ta kama a Adamawa
Masu garkuwa da mutane Hoto: SaharaReporters
Asali: UGC

Hotunan masu garkuwa da mutane 23 da makamansu da rundunar 'yan sanda ta kama a Adamawa
Makaman masu garkuwa mutane da rundunar 'yan sanda ta kama a Adamawa Hoto: SaharaReporters
Asali: UGC

Kwashinan, wanda aka mayar jihar kwanan nan, ya ce zai yi yaki da ta'addanci da 'yan ta'adda a Adamawa.

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa aka bawa hammata iska a kan gawar mahifiyar Buratai

"Domin samun damar yakar 'yan ta'adda da ta'addanci, zan yi aiki bisa tsarin babban sifeton rundunar 'yan sanda.

"Amma, jami'an 'yan sanda ba zasu samu nasara ba idan basu samu hadin kan jama'a ba, musamman wajen samar da sahihan bayanai ga rundunar 'yan sanda," a cewarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng