Sarakuna: Maida Almajirai gidajensu ba tare da an yi masu gwaji ba ya na da hadari

Sarakuna: Maida Almajirai gidajensu ba tare da an yi masu gwaji ba ya na da hadari

- Sarakuna sun yi magana game da Almajiran da ake ta faman maidawa gida

- Majalisar Sarakunan Arewan ta ce yin hakan zai kara yada cutar COVID-19

A yau Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa wata majalisar sarakunan gargajiya ta roki gwamnatin tarayya ta hana yawo da ake ta yi da almajirai daga wannan jiha zuwa wannan jiha.

Majalisar sarakunan ta gargadi gwamnatin tarayya cewa yunkurin maida almajiran zuwa garuruwan da su ka fito zai taimaka wajen yaduwar COVID-19 a Arewacin kasar.

Shugaban majalisar sarakunan, Alhaji Samila Mohammed ne ya yi wannan kira a lokacin da su ka yi wata ganawar gaggawa da gwamnatin tarayya da majalisar PHC ranar Laraba.

Rahotanni sun bayyana cewa an yi wannan ganawa ne ta yanar gizo daga babban birnin tarayya Abuja. Shugaban majalisar ya ce yawo da ake faman yi da almajiran ya na da hadari.

KU KARANTA: Coronavirus: An kwantar da Sarkin Daura a asibitin Katsina

Sarakuna: Maida Almajirai gidajensu ba tare da an yi masu gwaji ba ya na da hadari
Wasu Sarakuna sun roki Buhari ya hana yawo da Almajirai
Asali: Depositphotos

“Mun damu da maida almajirai jihohinsu da ake yi ba tare da an yi masu gwajin kwayar cutar COVID-19 ba. Wannan aiki zai taimakawa yaduwar wannan cuta.” Inji Mohammed.

Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya ce yawon da ake yi da almajirai tsakanin jihohi ya sabawa dokar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sa na haramta zirga-zirga.

Mai martaba sarkin Jiwa, Alhaji Idris Musa ya nemi gwamnatin shugaba Buhari ta yi wani abu game da yadda ake bizne wadanda su ka mutu a sanadiyyar cutar Coronavirus a kasar.

Sarkin na kasar Jiwa ya fadawa gwamnatin tarayya cewa mafi yawan mutanen da su ke halartar jana’izar wadanda cutar ta kashe ba su sanya irin kayan da ake amfani da su na kariya.

Mai martaba Mai Kaltungo, Saleh Muhammed, ya roki gwamnati ta kafa wajen gwajin COVID-19 a Gombe. Ministan lafiya da darektan hukumar NPHDA sun halarci taron ta kafar gizo.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel