Gwamnatin Ekiti za ta hukunta Matar da ta saci hanya ta shigo mana Jiha - Kwamishina

Gwamnatin Ekiti za ta hukunta Matar da ta saci hanya ta shigo mana Jiha - Kwamishina

- Jihar Ekiti ta ce za ta hukunta wata Matar Soja da ta kai wa Mijinta ziyara

- An gano wannan mata ta na da dauke da COVID-19 bayan ta isa Jihar Ekiti

Wata Baiwar Allah da yanzu ta ke jinyar COVID-19 a daya daga cikin dakunan da ake killace masu dauke da wannan cuta ta na jiran a kama ta da laifi da zarar ta murmure a jihar Ekiti.

Gwamnati ta haramta tafiya tsakanin wata jiha zuwa wata a halin yanzu domin takaita yaduwar cutar COVID-19. Ita wannan mata ta yi watsi da wannan doka, ta kama hanyar Ekiti.

Wannan mata ta saci hanya ne tun daga jihar Katsina, ta isa Ekiti domin ta ga mijinta wanda soja ne da ke aiki a jihar. Gwamnatin Ekiti ta ce wannan mata za ta yabawa aya zakinta.

Premium Times ta ce bayan wannan mata ta isa wurin mai gidan na ta ne sai ya fahimci cewa ta na fama da alamun rashin lafiya, a karshe aka tabbatar ta na dauke da Coronavirus.

KU KARANTA: COVID-19: Gwamnan Ekiti ya ragewa wasu Ma'aikata albashi

A ranar Laraba, 6 ga watan Mayu, gwamnatin jihar Ekiti ta bakin kwamishinar lafiya ta ce bayan an yi wa wannan mata gwaji ne aka gano cewa ta kamu da kwayar cutar da ake gudu.

Kwamishinar ta ce: “Ko da mijinta ne ya sanar da mu, ya sabawa dokar jihar Ekiti kuma ma’aikatar shari’a za ta dauki matakan da su ka dace a kan ta a lokacin da ya kamata.”

Dr. Mojisola Yaya-Kolade ta yi wannan jawabi ne a garin Ado-Ekiti. Kwamishinar ba ta bayyana matakin da za a dauka game da wannan mata da ta kawowa jihar Ekiti wannan cuta ba.

Yaya-Kolade ta kuma bayyana cewa wasu mutane bakwai da su ka shigo jihar daga Kano da Oyo sun shiga hannun hukuma. Kwamishinar ta ce yanzu an killace duk wadannan mutane.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel