Abdullahi Gadon-Kaya ya bada shawarar yadda za a bude Masallatai a Ranakun Juma’a

Abdullahi Gadon-Kaya ya bada shawarar yadda za a bude Masallatai a Ranakun Juma’a

- Abdullahi Umar Gadon Kaya ya na so a bar Jama’a su rika yin sallar Juma’a

- Malamin ya ce idan za a iya fita kasuwa, za a iya kyale Musulmai su yi sallah

- Sheikh Gadon Kaya ya ce akwai hanyar da za a bi wajen takaita sallar Juma’a

Ganin halin da aka shiga na zaman kulle na makonni wanda har ta kai ba a iya fita sallar jami’i a jihohin Najeriya da-dama, malamai sun fara fitowa su na neman a ba su damar yin ibada.

Sheikh Abdullahi Umar Gadon-Kaya ya roki gwamnatocin da su bude masallatai domin a koma sallar Juma’a. Malamin ya roki a ba su dama daga cikin kwanakin da ake badawa a fita.

Abdullahi Umar Gadon-Kaya ya yi wannan roko ne da babbar murya wajen wani karatu da ya yi a garin Kano. Shehin ya na ganin idan an hallata zirga-zirga, za a iya kyale sallar mutane.

Sheikh Gadon-Kaya ya ke cewa sai a kafa dokoki da sharudan da za a bi wajen yin sallar jami'in. A cewarsa za a iya amfani da ‘yan agaji wajen ganin kowa ya rufe fuskarsa a masallaci.

Bayan rufe fuska da tsummar kariya, malamin addinin ya ke cewa za a iya hana kowa shiga cikin masallaci har sai daf da lokacin da za a fara hudubar juma’a, domin a kare lafiyar al’umma.

KU KARANTA: Shekau ba za iya sa ni in yi shiru ba - Mai binciken Boko Haram

Gadon-Kaya ya ce limamai za su iya takaita huduba ta yadda za a yi sallah, a idar a cikin minti 20 zuwa 30. Shehin ya ce limamai sun sa hanyar da za su bi domin ayi maza a bada sallah.

Malamin ya ce za a iya bada tazara a cikin masallatai ta yadda ba za a samu cakuduwar masu ibada ba. Ya ce abin na yi masa takaici ganin yadda aka dade ba a iya yin sallar juma’a ba.

Tun da ana samun ranakun yin zirga-zirga a kasuwanni da bankuna ayi cefanen kayan amfani da na abinci, babban malamin ya roki gwamnati ta saki hanya a ranar Juma’a ayi sallah.

Wannan malami ya ke cewa wannan shawara da ya ke ba hukuma fahimtarsa ce, ya kuma nemi ayi masa kyakkyawan zato. A cewarsa sallar Juma’a tamkar larurar fita neman abinci ce.

A wannan lokaci da ake fama da annobar COVID-19, Gadon-Kaya ya ce su na bin duk sharudan lafiya da dokokin da aka kafa, sai dai ya roki a ba musulmai wannan dama ta rana guda.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel